'Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun sace 'yan ƙasar waje da ke aikin layin dogo na Legas zuwa Ibadan

'Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun sace 'yan ƙasar waje da ke aikin layin dogo na Legas zuwa Ibadan

  • Wasu yan bindiga sun tare wasu 'yan china da ke aikin layin dogo sun yi awon gaba da su
  • Yan bindigan sun bindige dan sandan da ke bawa yan chinan kariya kafin su yi awon gaba da su
  • Rundunar yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kuma tura jami'ai su bi sahunsu

An kashe wani jami'in dan sanda sannan an sace wasu yan kasar China su hudu da ke aiki a layin dogo na Legas zuwa Ibadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ruwaito cewa yan bindigan sun labe ne a kan iyakar Adeaga/Alaagba wani gari da ke kan iyakar jihohin Oyo da Ogun a ranar Laraba.

Tambarin yan sandan Nigeria
Tambarin yan sandan Nigeria. Hoto: Vangaurd
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Rashin tsaro: Mazauna wasu unguwanni a Zaria sunyi Sallar Al-Ƙunuti kan 'yan bindiga

Yan bindigan sanye da bakaken kaftani sun kutsa wurin da ake aikin layin dogon a kauyen Adeaga/Alaagba da ke karamar hukumar Odeda a jihar Ogun.

Vanguard ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da afkuwar lamarin a safiyar ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa rundunar ta tura jami'anta domin su bi sahun maharan.

Ya ce:

"Eh, da gaske ne abin ya faru a jiya Laraba. Wadanda aka sace yan kasar China ne da ke aiki a tashar jirgin kasa da ke Alaagba kusa da Kila.

KU KARANTA: Ana bada tukwicin tabar wiwi ga mutane don su yarda a musu allurar rigakafin korona a Amurka

"Yan bindigan sun kai musu hari a lokacin da suke hanyar zuwa can. An kashe dan sandan da ke basu kariya.
"Mun fara bincike tun jiya (Laraba), muna bin sahun mutanen da fatan za mu kama su.
"Mun tura jami'anmu su bi sahunsu kuma muna fatan da izinin Allah za mu gano su."

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel