Rashin tsaro: Mazauna wasu unguwanni a Zaria sunyi Sallar Al-Ƙunuti kan 'yan bindiga

Rashin tsaro: Mazauna wasu unguwanni a Zaria sunyi Sallar Al-Ƙunuti kan 'yan bindiga

  • Mutane a garin Zaria a jihar Kaduna sunyi addu'a ta musamman na neman tsarin Allah daga yan bindiga da sauran bata gari
  • Tanimu Abubakar, daya daga cikin malaman da suka jagoranci addu'ar ya ce yin addu'a suna ce ta Manzon Allah (SAW)
  • Malamin ya shawarci gwamnati ta dauki jami'an tsaro sannan ta basu kayan yaki da laifuka na zamani

Malaman addinin musulunci da mazauna garin Zaria, a ranar Laraba, sun yi addu'a ta musamman domin neman Allah ya kawo musu dauki game da kallubalen tsaro da ke adabar masarautar da jihar, New Nigerian ta ruwaito.

Daruruwan mutane sun hallarci addu'ar da aka yi ta musamman a filin sallar Idi na Kofar-Gayan Low Cost a Zaria.

Al'ummar musulmi na sallah
Al'ummar musulmi yayin da suke sallah. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zanga-Zanga ta ɓarke gidan yari yayin da gandireba ya bindige wani baƙo har lahira

Daya daga cikin wadanda suka jagoranci taron addu'ar, Tanimu Abubakar, ya ce addu'ar da suka kira ya yi dai-dai da koyarwar Manzon Allah (SAW) da ya koyar da musulmi su rika yin addu'o'i idan fitina ta same su.

Ya kara da cewa za a cigaba da yin addu'o'in a masallatai a jihar.

Malamin, ya kuma shawarci gwamnati ta dauki karin jami'an tsaro ta kuma tura su a wurare da suka dace a jihar domin dakile kallubalen rashin tsaron.

Ya bukaci gwamnati ta yi amfani da fasahar zamani ta kuma tallafawa jami'an tsaro kayan leken asiri na zamani domin basu damar magance bata garin.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC ya sake galaba kan ɗan takarar PDP a kotun ɗaukaka ƙara a Ondo

Ya kuma ce baya goyon wadanda ke kira da gwamnati ta bawa yan Nigeria daman rike bindigu yana mai cewa daga karshe hakan ba zai zama alheri a gare mu ba.

A baya bayan nan an rika kai hare-hare a wurare daban-daban a masarautar ta Zazzau inda aka rika sace mutane da dabobi.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: