Kasar Saudiyya Ta Yanke Wa Wani Matashi Hukuncin Kisa Kan Laifin da Ya Aikata Tun Yana Yaro

Kasar Saudiyya Ta Yanke Wa Wani Matashi Hukuncin Kisa Kan Laifin da Ya Aikata Tun Yana Yaro

  • Saudiyya ta yanke wa wani mutumi mai suna, Mustafa Hasheem Al-Darwish, hukuncin kisa
  • Hukumomi a ƙasar sun kama mutumin ne tun shekarar 2015 da zargin yana da hannu a wata zanga-zangar ta'addanci
  • Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun bayyana cewa laifukan da ake zargin mutumin ya aikata, yayi su ne tun yana ɗan shekara 17

Ƙasar saudiyya ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa kan zargin kitsa zanga-zangar ta'addanci da wasu laifuffuka a ƙasar.

BBC ta ruwaito cewa ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun bayyana cewa, laifin da ƙasar ke zargin mutumin da shi ya aikata su ne tun yana ɗan shekara 17.

KARANTA ANAN: Cikakke Bayani: INEC Ta Bayyana Sabon Adadin Runfunan Zaɓe a Najeriya, Ta Soke Wasu 746

Sai-dai hukumomin Saudiyya sun yanke wa, Mustafa Hashem al-Darwish, hukuncin kisa bayan tabbatar da ya aikata laifin da ake zarginsa da shi.

Saudiyya ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa
Saudiyya Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Kisa Kan Laifin da Yayi Tun Yana Yaro Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

Tun a shekarar 2015 ne ƙasar Saudiyya ta damƙe, Mustafa Hasheem, wanda mabiyin mazahabar shi'a ne, waɗanda suke tsiraru a ƙasar.

A baya hukumomin ƙasar saudiyya sun bayyana cewa sun daina yanke hukuncin kisa a kan ƙananan yara waɗanda basu cika shekara 18 ba.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun yi watsi da hukuncin Saudiyya

Ƙungiyar Amnesty International, mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adama, tace wanda ake zargin ya janye amsa laifinsa da yayi tun farko, kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Gidaje a Jiharsa Saboda Masu Garkuwa da Mutane

A cewar ƙungiyar, Mustafa ya amsa laifin da ake zarginsa da shi ne saboda azaba da matsi da ya fuskanta a hannun Waɗanda ke tsare da shi.

Amma a ɓangaren yan uwansa kuwa, sun ce an yanke wa Mustafa wannan hukuncin ne saboda ya taba cacar baki da jami'an tsaron Saudiyya.

A wani labarin kuma Babban Dalilin da Yasa Ba Zamu Taɓa Rabuwa da Almajiranci a Arewa Ba, Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, yace gwamnonin arewa ba dagaske suke ba wajen ɗaukar mataki a kan kwararar almajirai a jihohinsu.

Gwamnan yace ya zama wajibi gwamnonin jihohi su haɗa kan su sun ɗauki matakin daƙile matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel