Kada Ku Yarda Yan Bindiga Su Kashe ku, Gwamna Ya Gargaɗi Yan Sanda

Kada Ku Yarda Yan Bindiga Su Kashe ku, Gwamna Ya Gargaɗi Yan Sanda

  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya roƙi jami'an hukumar yan sanda da su daina bari wasu bara gurbi suna kashe su
  • Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yaje ta'aziyya ga hukumar a hedkwatar ta dake babban birnin jihar, Owerri.
  • Yace gwamnatinsa ta gama duk wasu shirye-shirye domin inganta rayuwar iyalan waɗanda suka mutu

Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo, ya roki jami'an hukumar yan sanda da su daina bari wasu yan ta'adda na kashe su, kamar yadda punch ta ruwaito.

Gwamnan yayi wannan jawabi ne yayin da yakai ziyarar ta'aziyya hedkwatar hukumar yan sandan jihar dake Owerri.

KARANTA ANAN: Fulani Makiyaya Sun Kashe Mutum 2 Tareda Sace Wasu 6 a Enugu da Akwa Ibom

Gwamnan ya jajantawa hukumar kan kashe wasu daga cikin jami'anta tare da ƙona wasu caji Ofis a jihar cikin watanni kaɗan da suka gabata.

Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo
Kada Ku Yarda Yan Bindiga Su Kashe ku, Gwamna Ya Gargaɗi Yan Sanda Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Gwamnan yace: "Zan ƙara faɗa da babban murya, ku ne kaɗai kuke da hurumin rike bindiga a ƙasar mu. Ku daina bari wasu marasa tunani su rinƙa kashe ku, waɗanda doka bata basu hurumin riƙe bindiga ba."

"Ku daina bari suna kashe ku, ku kare kanku sannan ku kare al'ummar mu da dukiyoyin su."

Gwamna Uzodinma yayi alaƙawarin Inshora ga jami'an tsaron jihar

Gwamnan Hope Uzodimma, yace gwamnatinsa zata samar da wani tsarin inshora ga jami'an tsaron dake aiki a jihar Imo.

KARANTA ANAN: Yadda Zamu Fitar da Wanda Zai Gaje Ni a 2023, Gwamna Ganduje

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gama duk wasu shirye-shirye wajen ganin an inganta rayuwar iyalan jami'an tsaron da suka rasa rayuwarsu a cikin wannan yanayin.

Yace gwamnatin sa zata yi duk me yuwuwa wajen inganta ayyukan jami'an tsaro, kuma ba zata watsar da iyalan jami'an da suka mutu ba.

A wani labarin kuma NLC Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani Saboda Mafi Ƙarancin Albashi

Ƙungiyar kwadugo, NLC, ta sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani a jihar Nasarawa saboda jan ƙafa da gwamnati ke yi wajen aiwatar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata da kuma walwalarsu.

Shugaban NLC na jihar Nasarawa, Yusuf Iya, yace sun yanke shawarar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel