Sojoji sun kama matasa 73 tare da babura 47 a hanyarsu ta zuwa jihar Imo daga Nasarawa
- Wani rahoton sirri ya kai ga cafke wasu matasa 73 da ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Imo daga Nasarawa da babura 47
- Sojojin da ke aiki a runduna ta musamman ta Birged 72, da ke Makurdi, babban birnin jihar Benuwe ne suka aiwatar da rahoton
- Binciken wadanda ake zargin ya fara, yayin da aka tabbatar da ba a samu wani makamai a tare da su ba bayan da aka wargaza baburan
Sojoji na Runduna ta Musamman ta Birged 72, Sojojin Najeriya, da ke Makurdi a daren Litinin, 14 ga Yuni sun kama matasa 73 daga jihar Nasarawa a kan hanyarsu ta zuwa Imo.
A cewar wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta fitar, ta ce sojojin da ke aiki a kan rahoton tsaro ne suka cafke matasan majiya karfi wadanda aka loda a manyan motoci biyar.
KU KARANTA KUMA: Ban mutu ba, Tinubu ya bayyana yayin da ya isa Najeriya daga Dubai
Haka kuma an ga babura kirar Bajaj guda 47 tare da matasan. An ce motocin na daukar wasu ma'adanai daga jihar Filato zuwa wani kamfani da ke Fatakwal.
Gwamnatin Benue ta nuna damuwa, ta yabawa sojoji
Mataimakin gwamnan jihar Benuwe, Benson Abounu, wanda ya ziyarci barikin a ranar Talata, 15 ga watan Yuni ya yaba wa sojoji kan kamun.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Neja ya koka kan yadda 'yan bindiga suka hana karatu da noma a jiharsa
Ya nuna farin ciki cewa duk da kokarin gujewa kamun, sojoji sun sami nasarar cafke manyan motocin tare da kama mutanen.
Ya nuna mamakinsa kan yadda za a samu irin wadannan dimbin samarin daga jiha daya a tare zuwa jihar Imo mai fama da rikici.
Sojojin Najeriya sun bayyana yadda aka kamasu
Kwamandan runduna ta musamman ta Birgede 72, Laftanar Kanar AD Alhassan ya ce mutanen nasa sun yi aiki ne bisa rahoton tsaro.
Ya bayyana cewa suna samun rahoton cewa wasu manyan motoci na hanyar tafiya zuwa Makurdi sai suka yunkura don tare motocin nan take.
Kungiyar Arewa Ta Gargadi 'Yan Arewa Kan Zuwa Yankin Kudanci
A wani labari na daban, kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta gargadi ‘yan Arewa kan tafiya zuwa yankin Kudu maso Gabas a yanzu saboda halin da ake ciki na rashin tsaro.
Ta ba da shawarar cewa idan tafiyar ta zama dole, to a yi amfani da jami'an tsaro a ciki, Nigeria Tribune ta ruwaito.
Wannan ya na kunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban ACF na kasa, Cif Audu Ogbe, ya fitar a ranar Litinin.
Asali: Legit.ng