Labari mai zafi: Gwamnan Bauchi, Bala ya tsige SSG, COS, Kwamishinoni da masu bada shawara

Labari mai zafi: Gwamnan Bauchi, Bala ya tsige SSG, COS, Kwamishinoni da masu bada shawara

- Gwamnan jihar Bauchi ya bada sanarwar tsige duka Kwamishinoninsa

- Bala Mohammed ya kori duk wasu Mukarrabai da masu ba shi shawara

- Hadimai hudu kacal suka tsira daga wannan zazzaga da Gwamnan ya yi

A safiyar yau ne Gwamnatin jihar Bauchi ta fitar da sanarwar sallamar kusan daukacin kwamishinoni da masu ba gwamna Bala Mohammed shawara.

Kamar yadda sanarwar da ta fito daga ofishin mai taimaka wa gwamnan jihar Bauchi wajen yada labarai da hulda da jama’a, wasu hadimai hudu kacal suka tsira.

Malam Mukhtar Gidado ne ya fitar da takardar wannan sanarwa a shafinsa na Facebook dazu.

KU KARANTA: Yadda aka kusa tsige ni daga kujerar Minista - Bala Mohammed

“Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala A. Mohammed CON (Kauran Bauchi) ya amince da ruguza daukacin majalisar zartarwa da sauran masu mukamin siyasa.”

Daga ciki har da sakataren gwamnatin jihar (SSG), da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da dukkanin masu bada shawarwari na musamman face wadannan:

1. Mai bada shawara a kan harkar tsaro

2. Mai bada shawara a kan aiki da majalisar dokoki da tarayya

3. Mai bada shawara a kan inganta rayuwar jama’a

4. Mai bada shawara a kan yada labarai da hulda da jama’a

KU KARANTA: Twitter: Buhari na neman kauda hankalin mutane ne - Ortom

Labari mai zafi: Gwamnan Bauchi, Bala ya kori duka Kwamishinoni da masu bada shawara
An kori Kwamishinonin Bauchi Hoto: www.facebook.com/255929144867936
Asali: Facebook

Mukhtar Gidado a madadin gwamnan ya kara da cewa:

“Duka kwamishinoni su sallama wa sakatarorin din-din-din na ma’aikatunsu ayyukansu, SSG da COS da sauran hadiman ofishin gwamna su mika ayyukansu ga babban sakataren din-din-din na gidan gwamnati, wanda aka ba umarni ya tattara inda kayan gwamnati su ke."

Mai girma gwamna Bala Mohammed ya gode wa wadanda wannan mataki da aka dauka ya shafa kan irin hidimar da su ka yi wa jiha, ya yi masu fatan alheri a rayuwa.

Ana jita-jitar cewa Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya fara shirin ficewa daga jam’iyyar PDP.

Dazu kun ji cewa Sanata Ahmad Sani Yarima ya na nan a kan bakarsa na cewa babu wanda ya ce mulki zai bar Arewa a 2023, don haka zai yi takarar shugaban kasa a APC.

Ahmad Sani Yarima ya bayyana abubuwan da zai yi idan Jama’a su ka zabe shi a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel