Akwai Matsala: Kungiyar Arewa Ta Gargadi 'Yan Arewa Kan Zuwa Yankin Kudanci
- Kungiyar tuntuba ta arewa a Najeriya ta yi kira ga 'yan arewa da su kauracewa zuwa yankin kudanci
- Kungiyar ta bada shawari kan yadda tafiyar ya kamata ta kasance idan ta zama dole sai an yi
- Hakazalika kungiyar ta bayyana yadda lamarin tsaro ya lalace a yankin kudanci musamman kudu maso gabas
Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta gargadi ‘yan Arewa kan tafiya zuwa yankin Kudu maso Gabas a yanzu saboda halin da ake ciki na rashin tsaro.
Ta ba da shawarar cewa idan tafiyar ta zama dole, to a yi amfani da jami'an tsaro a ciki, Nigeria Tribune ta ruwaito.
Wannan ya na kunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban ACF na kasa, Cif Audu Ogbe, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce ta lura da yadda damuwa ta yi yawa game da hare-hare da kisan 'yan Arewa mazauna da kuma maziyarta a yankunan Kudu, musamman Kudu maso Gabas.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Dole Masu Rubuta Jarrabawar JAMB Su Biya N700 Kudin 'Mock'
Wani yankin sanarwar na cewa: “Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) a yanzu tana ba da kyakkyawar shawara ga duk 'yan arewa da ke da niyyar zuwa Kudu maso Gabas.
“’Yan Arewa su auna muhimmanci da wajibcin irin wadannan tafiye-tafiye. Sai dai idan irin wadannan tafiye-tafiye suna da mahimmanci kuma suna da yanayi na tilas, kamar al'amuran rayuwa da mutuwa, sabanin haka bai kamata a yi su ba.
“Kuma idan tafiyar ta kama dole, matafiyi ya dauki duk matakan tsaro a cikin zirga-zirgarsa yayin da yake can, gami da cudanya da jami’an tsaro a wuraren zama/wuraren da za a ziyarta."
Lamurran tsaro na kara tabarbarewa a yankunan kudu, musamman yankin kudu maso gabas, lamrin da ya kai da zubar da jinane da dama ciki har da na wani gogaggen dan siyasa, Ahmed Gulak a karshen makon da ya gabata.
Jaridar Cable ta ruwaito yadda wasu tsagerun 'yan ta'adda suka hallaka Ahmed Gulak akan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama a garin Owerri ta jihar Imo aranar Asabar.
KU KARANTA: CSO Ta Yi Fatali da Kudurin Soke NYSC, Ta Bayyana Dalilanta
A wani labarin na daban, Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar, ya ce wadanda ke neman a soke shirin yiwa kasa hidimi na NYSC ba sa nufin Najeriya da alheri.
Ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin wasu zababbun mambobin NYSC na rukunin 'A' diba na 2 da aka tura jihar Sokoto a fadarsa da ke Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.
Maganar ta sarkin Musulmi martani ne ga yunkurin majalisar wakilai na soke shirin NYSC kwata-kwata a kasar duba da wasu dalilai da suka bayyana, jaridar Punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng