Tafiyar Tinubu ta na ta karfi; Magoya-baya sun dura Abuja da hotunan takara a 2023

Tafiyar Tinubu ta na ta karfi; Magoya-baya sun dura Abuja da hotunan takara a 2023

  • Hotunan Bola Tinubu sun fara yawo a wasu wurare a Birnin Tarayya Abuja
  • Magoya-bayan ‘Dan siyasar su na cigaba da rokonsa ya nemi takara a 2023
  • Har yanzu tsohon Gwamnan na Legas bai fito, ya ce yana neman mulki ba

Wasu masoyan jagoran jam’iyyar APC a kudancin Najeriya, Asiwaju Ahmed Tinubu, sun shigo birnin Abuja dauke da hotunan neman takararsa a 2023.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Litinin 14 ga watan Yuni, 2021, cewa magoya-bayan tsohon gwamnan na jihar Legas sun cika gari da hotunansa.

A ranar Lahadi wadannan mutane su ka shiga lika hotunan neman takarar shugaban kasar Bola Tinubu a wuraren da aka san zai dauki hankalin jama’a.

KU KARANTA: Buhari ya yi wa Tinubu hannun-ka mai sanda game da neman mulki

Daga cikin wuraren da hotunan na Bola Tinubu suka shiga akwai highbrow Maitama District, Central Business District, da kuma sakatariyar APC.

An ga an rubuta “TinubuNe”, ko kuma “Happy Democracy Day, Tinubu Advocates Group,” da “Jagaban Nigeria” da dai sauransu a jikin hotunan.

Legit.ng ta samu labari an rangada waka mai taken TinubuNe wanda yanzu haka ta fara yawo a kafofin sadarwa na zamani domin yi wa Tinubu kamfe.

Ko da cewa akwai sauran lokaci kafin a shiga yakin neman zaben 2023, wasu sun hakikance a kan ganin ‘dan siyasar ya fito neman kujerar shugaban kasa.

KU KARANTA: An sauke Shugaban jam'iyyar APC na jihar Filato

Tafiyar Tinubu ta na ta karfi; Magoya-baya sun dura Abuja da hotunan takara a 2023
Bola Tinubu a zaben Ondo Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

Shugaban wata kungiya mai suna, Disciples of Jagaban, Abdulhakeem Alawuje, ya yi magana da ‘yan jarida, ya ce burinsu shi ne Tinbu ya gaji Buhari.

“Muna goyon bayan Bola Tinubu, muna rokon shi ya fito neman shugaban kasa a zaben 2023 saboda cigaban kasa da ‘yan Najeroya." Inji Alawuje.

“Za ku yarda da ni cewa Tinubu ya yi kokari sosai wajen cigaban kasar nan. Mun san yadda ya dage wajen ganin Muhammadu Buhari ya yi mulki.”

Kuna da labari cewa an yi tir da Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a dalilin murje hoton tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da ya yi.

Abdullahi Ganduje ya bi ta kan wani hoton Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron APC. Har wasu 'yan APC suna ganin gwamnan bai kyauta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel