Rashin tsaro: Ba zai yiwu ka mayar da aikinka wuyan jihohi ba, Gwamna Wike ga Buhari
- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi zargin cewa gwamnonin APC sukan ruga wurin Shugaba Buhari don neman taimako kan rashin tsaro
- Gwamna Wike ya bukaci 'yan Najeriya da su kwatanta tsakanin gwamnonin APC da na PDP wadanda suka fi nuna kwazo a wannan yankin
- Wike ya kuma yi kira ga Buhari da ya aiwatar da aikinsa na kundin tsarin mulki na tabbatar da tsaro ga dukkan ‘yan kasar
Gwamna Nyesom Wike na Ribas ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi aikin da kundin tsarin mulki ya ba shi na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.
Gwamnan ya lura cewa a matsayisa na babban kwamandan rundunar sojin Najeriya, babban aikin Shugaba Buhari shi ne kare dukkan ‘yan kasa a kowace jiha, jaridar The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Watanni 3 bayan sasanci, Oshiomhole ya sake komawa rikicin siyasa da Obaseki
“Ya Shugaba, kai ne Babban-kwamandan rundunar Sojojin Tarayyar Najeriya. Ka nada Sufeto-Janar na 'yan sanda (IG), ka nada Shugaban hafsoshin Soja, Shugaban Sojojin Ruwa, Kwamishinan' Yan sanda (CP), Daraktan Sashen Kula da Harkokin Jiha (DSS) da sauran shugabannin tsaro. Wanne muka nada? Ta yaya mutanen da Shugaban Kasa ya nada za su kasance a karkashina? "
Wike yayi wannan bayanin ne a ranar Talata, 15 ga watan Yuni, yayin kaddamar da titin Odufor-Akpoku-Umuoye a karamar hukumar Etche na jihar, jaridar The Cable ma ta ruwaito.
Ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su yi la’akari sosai tsakanin ayyukan gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da na All Progressives Congress.
KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APGA ta kori Victor Oye a matsayin shugaba, ta kuma sanar da madadinsa nan take
Wike ya zargi gwamnoni daga jam’iyya mai mulki a matsayin wadanda ke yawan rugawa wajen shugaban kasa don neman taimako yayin da ‘yan fashi ke kai hare-hare a jihohin su.
Kalmominsa:
“Kamata ya yi Shugaban kasa ya fito fili ya ce, gwamnonina na APC, ku daina damuwa da ni. Ku koma jihohin ku sannan kuyi aikinku. A kan haka, ina goyon bayansa."
Ku daina jira sai na zo na magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari ga gwamnoni
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnoni da su daina jiransa don warware duk wata matsala da suke fuskanta, yana mai cewa ya kamata su dakatar da kai hare-haren makiyaya a jihohinsu, Sahara Reporters ta ruwaito.
Jihohi da yawa na fuskantar munanan hare-hare kan al'ummomi, inda ake fama da rikici ta fuskoki da dama ciki har da na makiyaya, wanda yasa ake matsa wa Shugaban kasa a matsayinsa na Babban Kwamandan sojin kasar da ya kawo dauki.
Kasancewarsa Bafulatani, da yawa daga yankunan kudancin Najeriya sun zarge shi da nuna son kai da rashin son magance hare-hare daga makiyaya, wadanda kuma galibi Fulani ne.
Asali: Legit.ng