Buhari zai ziyarci Borno, zai kaddamar da gidaje 4,000 na 'yan gudun hijira, Zulum
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Borno domin kaddamar da gidaje 4,000 na 'yan gudun hijira
- Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya ce shugaban kasan zai kai ziyarar kwana daya a ranar Alhamis
- Zulum ya bukaci 'yan jihar da su fito domin tarbar shugaban kasan wanda ya amince da kafa injin samar da wutar lantarki a jihar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci garin Maiduguri dake jihar Borno a ranar Alhamis na kwana daya, inji Gwamna Babagana Umara Zulum.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a yammacin ranar Talata a gidan gwamnatin jihar dake Maiduguri inda yace shugaban kasan zai duba yanayin halin da tsaron yankin arewa maso gabas yake ciki, Channels TV ta ruwaito.
A yayin ziyarar, ya ce shugaban kasan zai kaddamar da gidaje 4,000 wadanda suke daga cikin aikin gidaje na gwamnatin tarayya tare da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar.
KU KARANTA: Asari Dokubo: Abinda Fani-Kayode ya sanar da ni yayin da Nnamdi Kanu ya turo shi wurina
KU KARANTA: Twitter ta rubutowa FG wasika, tana bukatar a tattauna kan dakatar da ita
"Shugaban kasa zai kaddamar da kashi na farko na gidaje 10,000 wanda ya amince tare da daukar nauyi domin dawowar 'yan gudun hijira."
Kamar yadda gwamnan yace, aikin gidajen a Borno shine mafi girma a bangaren tallafin gidaje da gwamnatin tarayya tayi a jihar, Channels TV ta ruwaito.
A don haka yayi kira ga mazauna garin da su fito kwan su da kwarkwata wurin maraba da shugaban kasan a jihar.
Shugaba Buhari ya amince da kafa injin samar da wutar lantarki a Borno
Ya tunatar da jama'ar jihar yadda shugaban kasan ya amince da kafa injin samar da wutar lantarki na NNPC a jihar Borno domin shawo kan matsalar wuta.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa sauran ayyukan da shugaban kasan ya amince dasu a jihar yayi hakan ne domin yadda ya damu da damuwar jama'a a jihar.
A wani labari na daban, ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce Twitter da mamallakinta, Jack Dorsey, suna da alhaki kan asarar da kasar nan ta tafka a yayin zanga-zangar EndSARS, daily Niegrian ta ruwaito.
Ministan ya sanar da hakan ne yayin da ya zanta da gidan rediyo Najeriya a wani shiri na ranar Talata.
Mohammed wanda ya zargi Jack Dorsey da tara kudin gudumawar ta Bitcoin domin daukar nauyin zanga-zangar, ya ce an yi amfani da Twitter wurin rura wutar bala'in.
Asali: Legit.ng