Babbar Magana: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Gidaje a Jiharsa Saboda Masu Garkuwa da Mutane

Babbar Magana: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Gidaje a Jiharsa Saboda Masu Garkuwa da Mutane

  • Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun yayi alƙawarin rushe duk wani gida da aka kama masu garkuwa na boyewa a cikinsa
  • Gwamnan yace ba zai yuwu mutanen da suka hana zaman lafiya a jiharsa kuma su samu mafaka a cikinta ba
  • Ya kuma gargaɗi masu gidajen haya akan su tabbatar sun san mutum sosai kafin su bashi hayar gidan su

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, ya sha alwashin zai rushe duk wani gida da aka gano masu garkuwa suna buya a cikinsa, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Abun Tausayi: Iyayen Ɗaliban Islamiyya da Aka Sace Neja Sun Fara Bin Masallatai, Coci Suna Roƙon Kuɗi

Gwamnan yace ba zai yuwu mutanen da suka hana jama'a zaman lafiya kuma ace suna samun wurin ɓoyewa ba.

Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun
Babbar Magana: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Gidaje a Jiharsa Saboda Masu Garkuwa da Mutane Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamna Abiodun ya roƙi al'ummar jihar musamman masu gidajen haya, su tabbatar sun san waɗanda suke baiwa gidajen su.

Gwamnan yayi wannan gargaɗi ne yayin da yake jawabi a wurin wani taron kiristoci karo na 11 a Yewa, jihar Ogun.

KARANTA ANAN: Babban Dalilin da Yasa Ba Zamu Taɓa Rabuwa da Almajiranci a Arewa Ba, Ganduje

Wannan ba shine karon farko da gwamnan yayi gargaɗi ba

Wannan ba shine karon farko da gwamnan Ogun yayi wannan gargaɗi ba na rushe duk wani gida da masu garkuwa ke amfani da shi.

A shekarun baya gwamnan yayi wannan gargaɗi, inda har yayi barazanar kama mamallakin gidan, wanda ya baiwa baragurbi maɓoya a gidansa.

A wani labarin kuma Kada Ku Yarda Yan Bindiga Su Kashe ku, Gwamna Ya Gargaɗi Yan Sanda

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya roƙi jami'an hukumar yan sanda da su daina bari wasu bara gurbi suna kashe su, kamar yadda punch ta ruwaito.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yaje ta'aziyya ga hukumar a hedkwatar ta dake babban birnin jihar, Owerri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel