Babban Dalilin da Yasa Ba Zamu Taɓa Rabuwa da Almajiranci a Arewa Ba, Ganduje

Babban Dalilin da Yasa Ba Zamu Taɓa Rabuwa da Almajiranci a Arewa Ba, Ganduje

  • Gwamna Ganduje yayi wani jawabi kan dalilin da yasa arewa ba zata rabu da kwaranyar almajirai ba
  • Gwamnan yace ya zama wajibi gwamnonin jihohi su haɗa kan su sun ɗauki matakin daƙile matsalar
  • Yace a wasu lokutan idan aka maida almajirai asalin jihohin su, sai m su riga jami'an gwamnati dawowa

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, yace gwamnonin arewa ba dagaske suke ba wajen ɗaukar mataki a kan kwararar almajirai a jihohinsu, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Karin Bayani: Yan Majalisar Wakilai Sun Tantance Sabon Hafsan Soji, Manjo Janar Farouk Yahaya

Yace rashin haɗin kai da aiki tare tsakanim gwamnatocin jihohi shike maida hannun agogo baya a ƙoƙarin da ake da daƙile kwararar yar almajirai.

Gwamnan Kano yayi magana kan almajiranci a arewa
Babban Dalilin da Yasa Arewacin Najeriya Ba Zata Taɓa Rabuwa da Matsalolin Almajiranci ba, Inji Ganduje Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Gwamnan ya faɗi haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar kwanan nan a jihar Kano.

Ganduje yace: "Almajiranci babbar matsala ce, abunda muke jira shine matakin da gwamnatocin jihohi ya kamata su ɗauka na hana kwararan almajirai daga wannan jihar zuwa wata."

KARANTA ANAN: Wani Gwamnan Arewa Ya Ƙaddamar da Sabbin Jami'an Tsaro Na Musamman a Jiharsa

Maida almajirai zuwa gidan iyaye. Su yan agamuwa da cikas, Ganduje

Haka kuma Ganduje yace rashin aiki tare da kuma haɗin kai tsakanin gwamnonin arewa, shine yake daƙile ƙoƙarin da ake yi na maida almajiran zuwa gidajen iyayen su.

Yace: "Kasancewar Kano cibiyar kasuwanci, hakan yasa tana da almajirai daga kowace jiha dake arewa da kuma wasu kasashe kamar Nijar da Chadi."

"Wasu lokutan idan aka maida almajirai zuwa asalin garuruwan su, sai su riga jami'an gwamnati dawowa, sabida jihar da aka maida su ba su ɗauki matakin da ya dace ba."

A wani labarin kuma Kada Ku Yarda Yan Bindiga Su Kashe ku, Gwamna Ya Gargaɗi Yan Sanda

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya roƙi jami'an hukumar yan sanda da su daina bari wasu bara gurbi suna kashe su, kamar yadda punch ta ruwaito.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yaje ta'aziyya ga hukumar a hedkwatar ta dake babban birnin jihar, Owerri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262