Da Dumi-Dumi: Najeriya Za Ta Buga Wa Kasar Gambia Kudade, Ba Sauran Kai Wa Turai

Da Dumi-Dumi: Najeriya Za Ta Buga Wa Kasar Gambia Kudade, Ba Sauran Kai Wa Turai

  • Gwamnatin kasar Gambia ta nemi Najeriya da ta fara buga mata kudaden kasarta nan gaba
  • A cewar kasar, ta amince da jajircewar Najeriya wajen sarrafa kudade da kuma kwarewarta
  • Kamfanin buga kudi a Najeriya tuni ya bayyana cewa, a shirye yake ya fara aikin bugawar

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya amince bisa ka'ida don buga kudin Dalasi na kasar Gambiya, Daily Trust ta ruwaito.

Legit ta tattaro cewa, Gwamnan Babban Bankin, Mista Godwin Emefiele, ya amince da shawarar buga kudin daga Gwamnan Babban Banki na kasar Gambiya, Mista Buah Saidy, wanda ya jagoranci wata tawaga da ta ziyarce shi a ranar Talata.

KU KARANTA: Gwamna Ya Ba da Umarnin a Kwashe Mabarata Zuwa Wurin Alfarma a Jiharsa

Mista Emefiele ya ce Najeriya na da karfin gaske a harkar buga kudi kamar yadda take bugawa tun a shekarun 1960 kuma “a shirye muke mu taimaka wajen buga kudinku. Za mu iya kasancewa da araha sosai ta fuskar tsadancewa,” in ji shi.

Da dumi-dumi: Najeriya za ta buga wa kasar Gambia kudade
Labari da dumi-dumi daga Legit.ng Hausa | Legit
Asali: Original

Tun da farko Gwamnan Babban Bankin na Gambia ya ce kasarsa na fama da karancin kudi sosai kuma suna son koyon yadda za su sarrafa kudinsu da suke bukata duk shekara suna masu jinjina tarin ilimi da gogewar Najeriya.

Ya ce a halin yanzu, sun bayar da umarnin a kwashe shekaru biyu ana harkar buga musu kudaden a kasashen waje amma suna duba yiwuwar yin hakan daga Najeriya idan Najeriya ta amince.

A nata bangaren, kamfanin buga kudi na Najeriya, Nigerian Security Printing and Minting Company Plc ya ce a shirye yake idan duk bangarorin biyu sun cimma matsaya.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya magantu kan batun yin ritayarsa daga siyasa

EFCC Ta Bayyana Yadda Ake Sace Kudin Najeriya da Bitcoin, Ta Kwato Miliyoyi

A wani rahoton na daban, Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumar ta kwato kimanin dala miliyan 20 da barayi a yanar gizo suka wawure.

Mista Bawa, ya bayyana haka ne yayin shirin ‘Sunrise Daily’ na Channels Tv, ya kara da cewa an adana kudaden a cikin asusun yanar gizo na hukumar EFCC, Punch ta ruwaito.

Babban Bankin Najeriya a watan Fabrairun 2021 ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kudi su gano mutane da kungiyoyin da ke musayar kudin Intanet tare da rufe dukkan wadannan asusun.

Hakanan ya bayyana cewa ma'amala da musayar kudade da biyan kudi ta hanyar kudaden intanet haramun ne a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.