Shugaban EFCC Ya Bayyana Tsarinsa Na Tabbatar da Ya Karar da Rashawa a Najeriya

Shugaban EFCC Ya Bayyana Tsarinsa Na Tabbatar da Ya Karar da Rashawa a Najeriya

Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) Abdulrasheed Bawa ya ce yana da kyakkyawan fata cewa hukumar ta EFCC za ta shawo kan matsalar cin hanci da rashawa a kasar.

Bawa ya fadi haka ne a ranar Talata yayin wata hira a shirin karin kumallo na gidan talabijin na Channels, Sunrise Daily, lokacin da aka tambaye shi ko cin hanci da rashawa ya mamaye shi.

“Eh saboda idan ka kalli lamarin, kusan ko ina akwai abubuwan da ke tattare da shi (rashawa). A'a, saboda ina da kyakkyawan fata za mu yi nasarar shawo kan matsalar cin hanci da rashawa a kasar nan.

KU KARANTA: Gwamna Ya Ba da Umarnin a Kwashe Mabarata Zuwa Wurin Alfarma a Jiharsa

Shugaban EFCC ya bayyana aniyarsa ta kwamushe dukkan 'yan rashawa a Najeriya
Shugaban Hukumar EFC, Abdurrasheed Bawa | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

“Ina da kyakkyawan fata kuma tare da kokarin gwamnati. Daya daga cikin mahimman ka'idojin gwamnatin nan shine yakar cin hanci da rashawa kuma mu a hukumar EFCC da sauran jami'an tsaro masu dauke da wannan nauyin… muna iyakar kokarinmu kuma muna takaita shi."

Za mu yi amfani da shugabannin addinai wajen yaki da rashawa a Najeriya

Shugaban na EFCC da yake karin haske kan matakan da za a dauka na dakile cin hanci da rashawa a kasar ya ce hukumar na hulda da shugabannin addinai.

“Najeriya kasa ce mai matukar riko da addini wanda hakan ne ya sa daya daga cikin batutuwan da muke yi a wayar da kan jama’a shine tattaunawa da shugabannin kungiyoyin addini.

"Nan ba da jimawa ba za mu fara tattaunawarmu da mabiya addinin Kirista da na Musulunci don sanya su cikin yaki da rashawa.

"Mun riga mun tsara littafi na musamman don hakan."

KU KARATA: Da Dumi-Dumi: Najeriya Za Ta Buga Wa Kasar Gambia Kudade, Ba Sauran Kai Wa Turai

A rahoton baya, Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumar ta kwato kimanin dala miliyan 20 da barayi a yanar gizo suka wawure.

Mista Bawa, ya bayyana haka ne yayin shirin ‘Sunrise Daily’ na Channels Tv, ya kara da cewa an adana kudaden a cikin asusun yanar gizo na hukumar EFCC, Punch ta ruwaito.

Babban Bankin Najeriya a watan Fabrairun 2021 ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kudi su gano mutane da kungiyoyin da ke musayar kudin Intanet tare da rufe dukkan wadannan asusun.

Hakanan ya bayyana cewa ma'amala da musayar kudade da biyan kudi ta hanyar kudaden intanet haramun ne a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel