EFCC Ta Bayyana Yadda Ake Sace Kudin Najeriya da Bitcoin, Ta Kwato Miliyoyi

EFCC Ta Bayyana Yadda Ake Sace Kudin Najeriya da Bitcoin, Ta Kwato Miliyoyi

  • Shugaban hukumar EFCC ya bayyana cewa, hukumar ta kwato dala miliyan 20 daga yanar gizo
  • Hukumar ta ce ta bude asusun yanar gizo ta dawo da irin wadannan kudade da aka sace daga Najeriya
  • Hakazalika shugaban ya yaba wa CBN bisa dakatar da amfani da kudaden intanet da ta yi a watan Fabrairu

Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumar ta kwato kimanin dala miliyan 20 da barayi a yanar gizo suka wawure.

Mista Bawa, ya bayyana haka ne yayin shirin ‘Sunrise Daily’ na Channels Tv, ya kara da cewa an adana kudaden a cikin asusun yanar gizo na hukumar EFCC, Punch ta ruwaito.

Babban Bankin Najeriya a watan Fabrairun 2021 ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kudi su gano mutane da kungiyoyin da ke musayar kudin Intanet tare da rufe dukkan wadannan asusun.

Hakanan ya bayyana cewa ma'amala da musayar kudade da biyan kudi ta hanyar kudaden intanet haramun ne a kasar.

KU KARANTA: Gwamna Ya Ba da Umarnin a Kwashe Mabarata Zuwa Wurin Alfarma a Jiharsa

Ana amfani da Bitcoin wajen sace kudin Najeriya, EFCC ta kwato miliyoyin daloli
Shugaban Hukumar EFCC, Abdurrasheed Bawa | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Da yake magana a ranar Talata, Bawa ya goyi bayan matakin na CBN, yana mai cewa ya taimaka wajen takaita hanyoyin da masu aikata laifi ke wajen fitar da kudaden da suka aikata laifi a kasar.

Shugaban na EFCC ya ce, “Kamar yadda yake a yau, babu wani wuri a duniya da ake sarrafa kudaden intanet. EFCC tana duba hanyar da mutane ke shigowa da kudin sata da karbar kudaden aikata laifi, damuwarmu kenan.

“Mun gani lokuta da dama inda masu aikata laifuka ta yanar gizo ke amfani da wannan hanyar don karbar kudadensu na aikata laifi.

"Kafin yanzu ya kasance ta hanyar hukumomin tura kudi kamar Gram Money da kuma tabbas Western Union. Yanzu sun tafi yanar gizo. Zasu damfari mutum.

“Zasu sami katunan kyauta, suyi musayarsu akan yanar gizon damfara, kuma zasu yi amfani da kudin don siyan kudaden intanet, kuma zasu iya turasu zuwa asusun yanar gizonsu, sannan kuma, ba shakka, zasu iya siyarwa kuma su sami kudin su.

“Kamar yadda yake a yau, muna da kimanin dala miliyan 20 na kudin intaner kamar yadda yake a kididdigar karshe da nake da shi saboda mun kirkiri namu asusun yanar gizon don dawo da kudaden intanet," Bawa ya bayyana.

Dangane da kirkirar asusun na yanar gizo, Bawa yace hakan bai taba faruwa ba a gwamnati inda yake cewa, "Ka san hakan bai taba faruwa ba amma mun kirkire shi, a yanzu muna dawo da wadannan kudaden laifuka ta wannan hanyar.

"Don haka, muna goyon bayan abin da CBN ta yi saboda ta takaita hanyoyin da wasu daga cikin wadannan masu laifi za su iya musayar abin da suke so kuma su sami naira daga gare ta."

KU KARANTA: Miyetti Allah Ta Fayyace Jita-Jitar Cewa Fulani Za Su Kai Hari Delta

A wani labarin, Wata kungiya a karkashin kungiyar yaki da cin hanci da rashawa da mutunci ta yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan nadin Mista Abdulrasheed Bawa, a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).

Ta hanyar nadin, Bawa mai shekaru 40 ya zama mafi karancin shekaru da ya shugabanci Hukumar, Vanguard News ta ruwaito.

Da yake maida martani kan nadin ta wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban kungiyar yaki da cin hanci da rashawa, Kwamared Prince Kpokpogri, ya bayyana zabar Bawa a matsayin mafi kyawun abin da ya faru a matakin shugabancin EFCC.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel