Ka fara tattara komatsanka yanzu, PDP ta aikawa gwamnan APC sakon barin kujerarsa

Ka fara tattara komatsanka yanzu, PDP ta aikawa gwamnan APC sakon barin kujerarsa

  • Jam'iyyar People's Democratic Party ta yi fatali da sauya shekar da gwamna Ben Ayade ya yi zuwa jam'iyyar All Progressives Congress
  • Shugaban jam'iyyar na kasa, Uche Secondus, ya dage cewa jihar Kuros Riba ta PDP ce duk da sauya shekar Ayade
  • Jam’iyyar adawar ta ci gaba da sukar manufofin gwamnatin Buhari, ciki har da dakatarwar da aka yi wa Twitter a kwanan nan

Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Uche Secondus, ya ba gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba wa’adin barin kujerar mulki.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Secondus a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni, ya fadawa Ayade ya fara tattara kayansa daga gidan gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Watanni 3 bayan sasanci, Oshiomhole ya sake komawa rikicin siyasa da Obaseki

Ka fara tattara komatsanka yanzu, PDP ta aikawa gwamnan APC sakon barin kujerarsa
Shugaban PDP tar da wasu jiga-jigan jam'iyyar Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP)
Asali: Facebook

Shugaban na PDP ya yi wannan bayanin ne yayin kaddamar da kwamitin rikon a hukumance tare da bayyana sabuwar sakatariyar jam’iyyar ta jihar (annex) a Calabar.

Ya ce tabbas Ayade na nadamar shawararsa na sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Secondus ya ce:

“Wannan sanarwa ce ta sallama zuwa ga gwamna Ayade, ya kamata ya fara tattara kayansa kuma mun san cewa yana nadamar shiga APC saboda gwamnoni da yawa suna dawowa cikin gwamnonin PDP 14 daga APC mai mulki.”

A cewar jaridar The Sun, jigon na PDP ya bayyana cewa jam’iyyar ta kuduri aniyar kwato mulki a matakin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Sabon kudiri: Dole Buhari da shugabannin da ke mulki su yiwa 'yan Najeriya jawabi kan halin da kasar ke ciki

Ya bayyana cewa PDP za ta sake fasalin kasar idan ta mulki Najeriya a matakin tarayya. Secondus ya kuma yi wa mazauna jihar alkawarin cewa jam’iyyar za ta kwato Kuros Riba.

A wani labarin, gwamnonin jihohin da aka zaba a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari kan shawarar da ta yanke na dakatar da shafin Twitter a Najeriya har sai baba ta gani.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa gwamnonin PDP a cikin sanarwar bayan taro da suka fitar a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni, a Uyo, jihar Akwa Ibom, sun ba da dalilan da yasa akwai bukatar a dage haramcin.

Gwamnonin sun kuma nuna tsoron cewa gwamnatin Buhari na iya zamewa cikin mulkin kama-karya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel