Gwamnonin PDP sun lissafa dalilai 5 da yasa akwai bukatar Buhari ya soke dakatar da Twitter

Gwamnonin PDP sun lissafa dalilai 5 da yasa akwai bukatar Buhari ya soke dakatar da Twitter

  • Gwamnonin PDP sun bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya janye haramcin da ya sanya kan Twitter
  • Sun ce soke Twitter da aka yi a kasar zai kara yawan marasa aikin yi domin matasa da dama sun dogara da kafar sadarwar ne don samun kudaden shiga
  • Har ila yau gwamnonin sun ce haramcin tamkar katange 'yan Najeriya ne daga cin moriyar yancin da kundin tsarin mulkin kasa ta basu

Gwamnonin jihohin da aka zaba a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari kan shawarar da ta yanke na dakatar da shafin Twitter a Najeriya har sai baba ta gani.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa gwamnonin PDP a cikin sanarwar bayan taro da suka fitar a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni, a Uyo, jihar Akwa Ibom, sun ba da dalilan da yasa akwai bukatar a dage haramcin.

KU KARANTA KUMA: Yadda Zamu Fitar da Wanda Zai Gaje Ni a 2023, Gwamna Ganduje

Gwamnonin PDP sun lissafa dalilai 5 da yasa akwai bukatar Buhari ya soke dakatar da Twitter
Wasu daga cikin gwamnonin PDP Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria
Asali: Facebook

Korafi a kan haramcin

1. Gwamnonin sun ce haramcin da aka sanya kan shafin na Twitter zai kara tabarbarewar matsalar rashin aikin yi a kasar, suna masu lura da cewa haramcin zai cutar da matasan Najeriya wadanda ba su da isassun damar samun aikin yi kuma sun kasance suna dogaro da Twitter don samun kudin shiga ta halal.

2. Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaba Buhari da ya sake duba haramcin don amfanin kasa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun yi alkawarin ceto Najeriya daga mulkin APC a zaben 2023

3. Gwamnonin sun bayyana cewa dalilan da gwamnati ta bayar na dakatar da shafin na Twitter sun kasance na ra’ayin kai.

4. A cewar gwamnonin, za a iya aiwatar da ka'idojin kafofin sada zumunta ne kawai a tsakanin dokokin da ke nan a kasa kan batun.

5. Gwamnonin sun bayar da hujjar cewa ana iya amfani da haramcin a matsayin wani yunƙuri na azabtarwa ko hana yan Najeriya cin moriyar haƙƙoƙin da tsarin mulki ya ba su.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa gwamnonin sun kuma nuna tsoron cewa gwamnatin Buhari na iya zamewa cikin mulkin kama-karya.

Wasu na bakin cikin ganin Buhari a raye yana magana, Garba Shehu

A wani labarin, Babban hadimi na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, a ranar Litinin, ya ce wasu mutane sun yi bakin cikin ganin Shugaba Muhammadu Buhari yana ‘rayuwa ta hakika’ a cikin hira da aka yi dashi a karshen makon da ya gabata.

Shehu ya fadi haka ne a shirin gidan talabijin na NTA mai taken ‘Good Morning Nigeria’.

A makon da ya gabata ne Buhari ya gabatar da hirar da aka yi da shi a gidajen talabijin na Arise TV da NTA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel