Sabon kudiri: Dole Buhari da shugabannin da ke mulki su yiwa 'yan Najeriya jawabi kan halin da kasar ke ciki
- Nan ba da jimawa ba ‘yan majalisun Najeriya na iya amincewa da wani sabon kudiri wanda zai tilastawa shugabannin kasa yin jawabi ga kasar kan halin da kasar ke ciki
- Idan har aka zartar da kudirin, 'yan majalisar dokokin na Najeriya ma za su iya tilasta shugaban ya yi magana idan ya gaza girmama dokar
- A cewar wanda ya dauki nauyin dokar, ya samo asali ne daga kin bayyana da Buhari ya yi a gaban Majalisar Dokoki ta Kasa a shekarar da ta gabata
A wani mataki da zai faranta zuciyar 'yan Najeriya da dama, majalisar wakilai na gabatar da wani babban shawara da zai sauya yadda shugabanni ke zantawa da 'yan Najeriya.
Kudirin wanda wani dan majalisa ya dauki nauyin sa, yana neman a tilastawa kowane Shugaban kasa mai ci ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya kan halin da kasar ke ciki, jaridar Punch ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Dasuki ya bayyana matsayarsa a kan neman takarar kujerar gwamnan Sakkwato a 2023
Da wannan kudirin, za a bukaci shugaba Buhari ko kuma wani shugaban da ke kan kujerar mulki ya yi jawabi a gaban hadadden taron Majalisar Kasa lokaci zuwa lokaci.
Idan suka ƙi yin wannan, za a ba Majalisar Dokoki ikon gayyatarsa.
Dan majalisar mai wakiltar mazabar tarayya ta Ethiope-East / Ethiope-West a jihar Delta, Mista Ben Igbakpa ne ya dauki nauyin kudurin.
KU KARANTA KUMA: Gwamnonin PDP sun lissafa dalilai 5 da yasa akwai bukatar Buhari ya soke dakatar da Twitter
An sanya wa dokar suna, 'Kudirin doka don yin tanadi kan Shugaban kasa yayi jawabi kan halin da kasa ke ciki da sauran batutuwa, 2020.'
Kudirin ya ce:
"Kaddara Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya ta zartar da shi kamar haka:
"Shugaban kasar zai yi jawabi a taron hadin gwiwar da aka ambata a kan wadannan batutuwa ciki har da amma ba a iyakance ba kan tsaron kasa, tattalin arziki, aiwatar da kasafin kudi, manufofin kasashen waje da adalci na zamantakewa."
Maganar canzawa Najeriya suna zuwa 'United African Republic' ta kai gaban Majalisar Tarayya
A gefe guda, mun ji cewa kwamitin da ke sauraron maganar yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawul ya karbi kudirin sauya sunan kasar nan.
Wani masani a kan sha'anin haraji, Adeleye Jokotoye, ya gabatar da kudiri a gaban wannan kwamiti da ke zama a Legas, a ranar 2 ga watan Yuni, 2021.
Kamar yadda jaridar Independent ta rahoto a jiya, abin da Adeleye Jokotoye yake so shi ne, a canza wa Najeriya suna zuwa kasar United African Republic.
Asali: Legit.ng