Watanni 3 bayan sasanci, Oshiomhole ya sake komawa rikicin siyasa da Obaseki

Watanni 3 bayan sasanci, Oshiomhole ya sake komawa rikicin siyasa da Obaseki

  • Akwai yiwuwar sabunta sabani tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da tsohon ubangidansa na siyasa Adams Oshiomhole
  • Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya zargi Obaseki da mayar da yankin Edo ta Arewa saniyar ware
  • Oshiomhole a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni, ya ce rashin kaddamar da zababbun mambobin majalisar dokokin APC 14 ba daidai ba ne

An zargi gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo da yin watsi da yankin Edo ta Arewa ta hanyar rashin kafa wani aiki ko guda a yankin.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ne ya yi wannan zargi a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni, yayin taron shugabannin jam’iyyar APC a mahaifarsa, a Iyamho, Edo ta Arewa.

KU KARANTA KUMA: Sabon kudiri: Dole Buhari da shugabannin da ke mulki su yiwa 'yan Najeriya jawabi kan halin da kasar ke ciki

Watanni 3 bayan sasanci, Oshiomhole ya sake komawa rikicin siyasa da Obaseki
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki Hoto: @godwinobasekiofficial
Asali: Facebook

An tattaro cewa tsohon gwamnan ya dawo da gwagwarmayar siyasar da wanda ya gaje shi kan rashin kaddamar da mambobin majalisar dokoki 14 da aka zaba a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Sai dai kuma, bikin rantsar da su ya tsaya cik saboda rikicin da ke tsakanin Oshiomhole da Obaseki kan tikitin takarar gwamna na jam’iyya mai mulki.

A cewar Oshiomhole, babu adalci ace ba a rantsar da zababbun ‘yan majalisar 14 ba yayin da sauran mambobi 10 masu biyayya ga Obaseki suka zauna a gidan Gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Dasuki ya bayyana matsayarsa a kan neman takarar kujerar gwamnan Sakkwato a 2023

Ya ce:

“Yan majalisa 14 da aka zaba a majalisar Edo a karkashin inuwar APC, har zuwa yanzu, ba a kaddamar da su ba. Amma, ba su yi zunubi ba.
“An hana su‘ yancinsu na a rantsar da su don wakiltar wadanda suka zabe su. Allah zai isar musu da adalci a hanyarsa kuma a ƙayyadadden lokacinsa. ”

Sai dai kuma, Obaseki a wani rahoto da jaridar The Cable ta fitar ya ce ba shi da ikon dawo da zababbun ‘yan majalisar.

Ya lura cewa mambobin majalisar 14 ba a hana su gudanar da ayyukansu ba, amma “sun ki yarda a rantsar da su”.

Dole in binciki satar N30bn a kwangilar ruwan da Oshiomhole su ka yi inji Gwamna Obaseki

A wani labarin, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi magana game da matakin da ya dauka na binciken aikin gwamnatin da ta shude ta Adams Oshiomhole.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Godwin Obaseki ya na cewa zai binciki kwangilar aikin ruwan shan da Adams Oshiomhole ya bada a kan Naira biliyan 30.

Da yake magana da magoya-baya a garin Benin wajen bikin da aka shirya wa Dan Orbih, gwamnan ya ce an tafka sata ta karkashin wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel