Dole in binciki satar N30bn a kwangilar ruwan da Oshiomhole su ka yi inji Gwamna Obaseki

Dole in binciki satar N30bn a kwangilar ruwan da Oshiomhole su ka yi inji Gwamna Obaseki

- Godwin Obaseki ya ce an sace kudin kwangilar ruwan da Adams Oshiomhole ya bada

- Gwamnan jihar Edo ya ce ya zama dole ya binciki yadda aka sulale da kudin al’umma

- Obaseki ya ce kwangilolin da Oshiomhole ya bada da yake ofis, sun fi na yanzu tsada

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi magana game da matakin da ya dauka na binciken aikin gwamnatin da ta shude ta Adams Oshiomhole.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Godwin Obaseki ya na cewa zai binciki kwangilar aikin ruwan shan da Adams Oshiomhole ya bada a kan Naira biliyan 30.

Da yake magana da magoya-baya a garin Benin wajen bikin da aka shirya wa Dan Orbih, gwamnan ya ce an tafka sata ta karkashin wannan aiki.

KU KARANTA: Oshiomhole ya soki aikin rajistar da shugaban APC ya kirkiro

Wasu mutane sun wawuri kudin da aka ware domin cigaban jihar (Edo) inji gwamna Godwin Obaseki.

“A matsayina na shugaban kwamitin tattalin arziki a wancan lokaci, na dage dole Edo ta cigaba, saboda haka na bada gudumuwar shekaru takwas a lokacina daga babban bankin Duniya da ‘yan kasuwa domin cigaban jihar, amma wasu su ka sace kudin.”

Ya ce: “Eh, ina cikin gwamnatin, amma bayan abin da na gani a rubuce, sai na zama kamar wani sakarai.”

“Lokacin da na ke shirya lissafin kudin gwamnatin, ban lura cewa wasu sun sace kudin da na ke ta faman tara wa ba. Dole mutane su yi bayani.” Inji Obaseki.

Dole in binciki satar N30bn a kwangilar ruwan da Oshiomhole su ka yi inji Gwamna Obaseki
Gwamnan Edo, Obaseki Hoto: @GovernorObaseki
Source: Twitter

KU KARANTA: Ba kullum ake kwana a gado ba inji Adams Oshiomhole

“Ba na son bincike amma na shiga tsaka mai-wuya saboda idan na duba kwangilolin da na bada a 2020, da wadanda aka bada shekaru 10 da su ka wuce, dole wasu su amsa tambayoyi.”

Gwamnan ya kara da cewa: “Dole a fada wa mutane gaskiya, mutanen Edo sun san cewa an bada kwangilar Dala miliyan 200, kuma an fitar da duka kudin.”

Ku na sane da yadda sabani ya shiga tsakanin Adams Oshiomhole da tsohon yaronsa, gwamna Godwin Obaseki. A dalilin haka ne gwamnan ya koma PDP.

A zaben jihar Edo da aka yi, Godwin Obaseki ya doke Osagie Ize-Iyamu wanda Adams Oshiomhole ya tsaida a jam’iyyar APC a kananan hukumomi 13 a cikin 18.

Masana su na ganin cewa farin jinin PDP, rikicin APC, gajiya da karfa-karfar Adams Oshiomhole, sun taimaka wa Obaseki wajen zarce wa a kan kujerar Gwamna.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel