Dasuki ya bayyana matsayarsa a kan neman takarar kujerar gwamnan Sakkwato a 2023

Dasuki ya bayyana matsayarsa a kan neman takarar kujerar gwamnan Sakkwato a 2023

  • Hon. Abdussamad Dasuki, kwamishinan kudi na Sakkwato yayi tsokaci kan batun tsayawarsa takarar gwamnan jihar a 2023
  • Dasuki ya bayyana cewa baya daga cikin wadanda za su nemi wannan kujera ta gwamna, saboda haka a cire sunansa a jerin
  • Ya bayyana cewa abunda ya fi mayar da hankali a kai yanzu shine nauyin kula da kudaden Sakkwatawa wanda Gwamna Tambuwal ya dora masa
  • Har ila yau kwamishinan ya bayyana yadda gwamnan jihar ya bunkasa tattalin arzikin jihar tun bayan da ya hau karagar mulki

Kwamishinan Kudi na jihar Sakkwato, Hon. Abdussamad Dasuki, ya ce shi ba ya cikin masu takarar neman kujerar gwamna a 2023.

Dasuki ya fadi haka ne a lokacin da ya bayyana a wani gidan rediyo inda ya yi magana a kan nasarorin da Gwamna Aminu Tambuwal ya samu, a matsayin wani bangare na raya ranar Demokradiyya ta 2021, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin PDP sun lissafa dalilai 5 da yasa akwai bukatar Buhari ya soke dakatar da Twitter

Dasuki ya bayyana matsayarsa a kan neman takarar kujerar gwamnan Sakkwato a 2023
Kwamishinan Kudi na jihar Sakkwato, Hon. Abdussamad Dasuki Hoto: Thisdaylive.com
Asali: UGC
Da yake amsa tambaya kan zaben gwamna na 2023 da kuma ko zai shiga takarar domin ya gaji Gwamna Tambuwal, Dasuki ya ce, “Ba na cikin takarar. Da fatan za a daina saka ni cikin masu takarar gwamna a 2023.”

Dasuki ya ce Allah ya bashi dama da har Gwamna Tambuwal ya daura shi a wani muhimmin aiki a matsayin Kwamishina don jan ragamar kudaden jihar tare da tabbatar da komai ya tafi daidai bisa adalci don amfanin mutanen Sakkwato.

Ba zan shagala da siyasar 2023 ba

Kwamishinan ya ce ya mayar da hankali kan wannan aiki da gwamnan ya rataya masa kuma siyasar 2023 ba za ta shagaltar da shi ba.

Dasuki ya yi kira ga duk masoya Sakkwato da su hada kai da Gwamna Tambuwal a kudurinsa na saita jihar tare da isar da romon dimokiradiyya ga mutane.

Da yake tsokaci game da cika shekaru biyu na wa’adin mulki na biyu na gwamnatin Tambuwal, Dasuki ya lura cewa ma’aikatarsa tana kan aikin kula da baitulmali tare da yin aiki don tabbatar da jihar Sakkwato ta kasance cikin koshin lafiya a bangaren kudi da ci gaba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun yi alkawarin ceto Najeriya daga mulkin APC a zaben 2023

Tambuwal ya karfafa tattalin arzikin jihar Sakkwato

Jaridar Thisday ta ruwaito cewa kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Tambuwal ya karfafa tattalin arziki, ya tsaftace tsarin biyan albashi, ya toshe baraka Sannan kuma ya saisaita kudaden jihar.

Ya ce gwamnatin Tambuwal kuma tana sauya Sakkwato ta zama mai wayayyiyar gwamnati tare da manufofi da aka tsara da kuma daidaita su bisa la'akari da bayanai da nazari.

Kwamishinan ya lura cewa ajandar sake fasalin Gwamna Tambuwal ta fara haifar 'ya'ya masu idanu.

Ya lura da fitowar Sakkwato a matsayin wanda ya fi kowa cin gajiyar shirin Bankin Duniya na Tallafin Kasafin Kudi, shirin SFTAS a matsayin daya daga cikin sakamakon sake fasalin jihar na gwamnatin Tambuwal.

Ganduje yayi tsokaci kan wanda zai gaji kujerarsa ta gwamna a jihar Kano

A wani labarin, mun ji cewa duk da raɗe-raɗin da ake yi kan wane ɗan takara APC zata tsayar a zaɓen gwamnan Kano na 2023. Gwamna Ganduje yayi magana kan yadda za'a fitar da magajin shi, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Hakanan gwamnan ya kuma yi tsokaci kan yadda APC zata fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa duk da jita-jitar da ake yaɗawa cewa za'a kai takarar wani yanki.

Yayin da yake amsa tambayoyi a taron manema labarai, Gwamna Ganduje na jihar Kano yace wakilan jam'iyyar APC ne zasu zabi wanda zai tsaya takara ƙarƙashin jam'iyya, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel