Maganar canzawa Najeriya suna zuwa 'United African Republic' ta kai gaban Majalisar Tarayya

Maganar canzawa Najeriya suna zuwa 'United African Republic' ta kai gaban Majalisar Tarayya

- Wani mutum ya kai kudirin canza sunan Najeriya wajen Majalisar Tarayya

- Adeleye Jokotoye ya na ganin kasar za ta fi kyau da United African Republic

- Jama’a suna ganin ba a nan mafitar ta ke ba, domin ba a canzawa tuwo suna

Jaridar Pulse ta rahoto cewa kwamitin da ke sauraron maganar yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawul ya karbi kudirin sauya sunan kasar nan.

Wani masani a kan sha'anin haraji, Adeleye Jokotoye, ya gabatar da kudiri a gaban wannan kwamiti da ke zama a Legas, a ranar 2 ga watan Yuni, 2021.

Kamar yadda jaridar Independent ta rahoto a jiya, abin da Adeleye Jokotoye yake so shi ne, a canza wa Najeriya suna zuwa kasar United African Republic.

KU KARANTA: Limamin Ka'aba ya ziyarci Zulum bayan ya ji yabon da ake yi masa

Da yake bayani a gaban kwamitin majalisar tarayyar, Adeleye Jokotoye, ya bayyana abin da ya sa yake ganin kasar ta na bukatar canjin suna a halin yanzu.

Jokotoye yake cewa turawan mulkin mallaka ne suka kakaba mana sunanmu na Najeriya, don haka zai fi kyau a koma wa sunan Jamhuriyyar tarayyar Afrika.

“A daidai na wannan lokaci a tarihinmu, ya wajaba mu canza sunanmu ta yadda zai yi tasiri a sabon kundin tsarin mulkin kasar.” Inji Adeleye Jokotoye.

A madadin United African Republic, wannan mutumi ya ce za a iya daukar sunan United Alkebulan Republic, saboda irin tarin al’ummar da ke kasar.

Maganar canzawa Najeriya suna zuwa 'United African Republic' ta kai gaban Majalisar Tarayya
'Yan Majalisar Tarayya Hoto: www.guardian.ng
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnati za ta rika bibiya dukiyar Jami’in kwastam a Najeriya

Mutane sun yi tir da wannan shawara a shafukan Twitter, inda wani Bawan Allah ya ce da zarar an nemi a kawo gyara a kasar nan, sai kurum a canza suna.

Real Ade King ya ce: "Matsalar Najeriya tun a ranar gini ne, ba a suna ba ne. Canza suna zuwa United African Republic, kamar lokacin da NEPA ta koma PHCN ne, hakan bai sa an samu wuta ba."

“Suna neman yi wa Najeriya wankan tsarki, menene kuma wani United African Republic?” inji Samuel Mba

Japeth J. Omojuwa ya na ganin don an ga kasashe irinsu UK, US da UAE suna da arziki, shiyasa aka bada shawarar Najeriya ta koma gamayyar kasar Afrika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel