Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun yi alkawarin ceto Najeriya daga mulkin APC a zaben 2023

Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun yi alkawarin ceto Najeriya daga mulkin APC a zaben 2023

  • Aminu Waziri Tambuwal ya ce za su karbe shugabancin kasa a zabe mai zuwa
  • Shugaban gwamnonin PDP ya yi wannan alkawari ne a Uyo, a jihar Akwa Ibom
  • Gwamnonin jihohin adawa sun hadu, za su yi zama na musamman a garin Uyo

Duka Gwamnonin jam’iyyar PDP sun sha alwashin cewa za su yi duk abin da ya kamata wajen ganin sun karbe kujerar shugaban Najeriya a zaben 2023.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto cewa shugaban gwamnonin PDP, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi wannan jawabi a garin Uyo, Akwa Ibom.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya sha wannan alwashi a ranar Lahadi yayin da ake shirye-shiryen zaman da gwamnonin PDP za su yi.

KU KARANTA: Buhari ya tsufa, wasu miyagu suna cin albasa da bakinsa - Kokori

Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya ce gwamnonin jihohin jam’iyyar PDP ba za su ba mutanen Najeriya kunya ba, wajen ganin sun karbe mulki a sama.

Ya ce: “Wadannan gwarazan jagorori na gwamnonin PDP a jihohinsu da kuma kwararrun siyasa, suna cin albarkacin addu’o’i, goyon baya da hadin-kanku.”

Gwamnan yake cewa a wajen ceto kasa, za su dage sai sun kai ga samun nasara a zabe mai zuwa. Jaridar Tribune ta fitar da rahoton wannan a ranar Litinin.

“Ubangiji na tare da mu, za mu dage a matsayinmu na shugabanni, mu yi abin da ya dace wajen ganin PDP ta karbe shugabancin kasar nan idan 2023 ta zo.”

Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun yi alkawarin ceto Najeriya daga mulkin APC a zaben 2023
Gwamna Aminu Tambuwal Hoto: Sokoto state Governor
Asali: Facebook

KU KARANTA: Bayan ya koma APC, Gwamna Umahi ya zargi PDP da kawo rashin tsaro

Gwamna Aminu Tambuwal ya yi kira ga jama’a, musamman shugabannin addini, su cigaba da sa Najeriya a addu’a, ganin halin rashin tsaro da ake fama da shi.

A karshe, ya ce: “Mu na bukatar addu’o’i. Ubangiji na nan domin ‘Yan Najeriya, Ba zai taba gajiya ba.”

Da yake na sa jawabin, gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya yi wa takwarorinsa a PDP lale maraba da zuwa Uyo, inda aka tarbe su a gidan gwamnati.

A shekarar bara ne ake zargin Gwamnoni Darius Ishaku, Aminu Tambuwal da Samuel Ortom su ka nemi kujerar shugaban Gwamnonin PDP, inda Tambuwal ya yi nasara.

Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal shi ne ya gaji Seriake Dickson wanda ya wa’adin mulkinsa ya cika a jihar Bayelsa. Hakan ya sa wannan karo kujerar da tawo Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel