Miyetti Allah Ta Fayyace Jita-Jitar Cewa Fulani Za Su Kai Hari Delta
- Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta nesanta kanta da ikirarin kai hari yankin kudanci
- Ta ce ba a san kungiyar da aikata irin wannan barna ba, don haka ba za ta fara shi a yanzu ba
- Hakazalika, ta yi martani ga batun shugaban kungiyar PANDEF kan batun kiwo sakaka a kasar
Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta nesanta kanta daga wata sanarwa da aka danganta da kungiyar, inda aka ce ta ba da wa’adin awanni 72 ga Jihar Delta don sauya dokokinta kan kiwo a sakaka, Channels Tv ta ruwaito.
A cewar Sakatare-janar na kungiyar ta MACBAN, Usman Baba-Ngelzerma, irin wannan bayanin da wasu boyayyun mutane ke yi suna yi ne kawai don haifar da rikici cikin al'umma.
Baba-Ngelzerma ya ce MACBAN amintacciyar kungiya ce da ke da fitattun mutane kamar Sarkin Musulmi a matsayin uba gareta don haka ba za ta taba yin wani abu da zai dagula zaman lafiyar kasar nan ba.
KU KARANTA: Tambuwal Ga ’Yan Najeriya: Ku Taya Mu da Addu’a, PDP Na Tsara Karbe Mulki a 2023
Da yake mayar da martani ga taron manema labarai da shugaban kungiyar Pan Niger Delta Forum (PANDEF) Cif Edwin Clark ya yi a baya, shugaban kungiyar ta MACBAN ya ce har yanzu matsayin kungiyar na batun kiwo a fili na nan daram.
Ya bukaci Gwamnonin Arewa da su tabbatar da dawo da duk hanyoyin kiwo a kasar nan, ya kara da cewa Fulani makiyaya suna da ‘yanci daidai da duk 'yan Najeriya kuma ba zai yiwu a mayar dasu saniyar ware ba.
Cif Edwin Clark ya caccaki ra'ayin dawo da tsarin burtali ga Fulani makiyaya
Dattijo kuma tsohon kwamishinan yada labarai na tarayya, Cif Edwin Clark, ya ce ba abin yarda ba ne ga Gwamnatin Tarayya ta yi kokarin nuna fin karfi ga gwamnatocin jihohi kan batun kiwo sakaka ba.
Da yake magana a ranar Litinin, Cif Clark ya ce Shugaba Mohammed Buhari ba shi da ikon sanya dokar kiwo sakaka ga jihohi.
Cif Clark na martani ga maganar shugaba Buhari a cikin wata hira da ya yi kwanan nan, inda ya ba da kyakkyawar amincewa ga ra'ayin Jamhuriya ta Farko wanda zai duba dawowar burtali da zai ba makiyaya damar bin hanyoyin da aka tsara a duk fadin kasar.
Wannan matakin bai yiwa 'yan Najeriya da yawa dadi ba, yayin da wasu ke ikirarin cewa dagewar barin kiwo sakaka ga makiyaya na da wata boyayyar manufa.
A martanin da ya mayar game da batun, Clark ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya dauki kansa a matsayin shugaban kasar Najeriya ba wai a matsayin shugaban kabilar Fulani ba.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta gurgunta Najeriya, PDP ta koka kan yawan cin bashi
A wani labarin, Biyo bayan barazanar da wata ƙungiyar Fulani mai iƙirarin jihadi ta yi na kai hari Asaba da kuma Agbor na jihar Delta.
Kwamishinan yan sandan jihar, Mr Ari Mohammed Ali, ya sha alwashin bada cikakken tsaro ga al'ummar yankunan, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
A wani jawabi da kakakin hukumar yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya fitar, yace:
"An jawo hankalim hukumar mu kan wani rahoto dake yawo, wanda wasu yan fulani dake ikirarin jihadi suka fitar mai taken 'Gargaɗin fulani yan jihadi,' sannan kuma aka liƙa shi a wurare da dama musamman Asaba da Agbor."
Asali: Legit.ng