Tambuwal Ga ’Yan Najeriya: Ku Taya Mu da Addu’a, PDP Na Tsara Karbe Mulki a 2023

Tambuwal Ga ’Yan Najeriya: Ku Taya Mu da Addu’a, PDP Na Tsara Karbe Mulki a 2023

  • Gwamnonin Najeriya karkashin jam'iyyar PDP sun yi taro don karbe mulkin APC a zaben 2023
  • Gwamnonin sun bayyana cewa, suna son fitar da wani tsari ne wanda zai basu damar karbar mulkin
  • Hakazalika sun bukaci addu'ar nasara daga bakin 'yan Najeriya domin kuwa Allah yana tare dasu

Gwamnonin da ke karkashin jam'iyyar PDP sun hadu a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom don yin shawarwari kan yadda za a tumbuke jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2023, Premium Times ta ruwaito.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, gwamnonin suka yi alkawarin samar da tsarin da jam'iyyar ke bukata don dawowa kan mulki a matakin tarayya a 2023

Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya yi wannan alkawarin a wata liyafa da gwamnatin jihar Akwa-lbom ta shirya, gabanin taron kungiyar a Uyo.

KU KARANTA: Karyane: Sojin Saman Najeriya Sun Karyata Jefa Bama-Bamai Kan Masu Daurin Aure

PDP na kitsa yadda za ta yi ta kifar da mulkin APC a zaben a 2023, in ji Tambuwal
Gwamnonin jam'iyyar PDP yayintattaunawa kan tsarin cin nasarar zaben shugaban kasa ta 2023 Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tambuwal ya ce gwamnonin PDP ba za su ba ’yan Najeriya kunya ba a aiwatar da burinsu na ganin jam’iyyar ta dawo kan mulki a 2023.

ya ce "Wadannan taurarin shugabannin gwamnonin PDP a jihohinsu da gogewarsu ta siyasa sun kafu ne da yardar Allah ta hanyar addu'o'inku, goyon baya da hadin kai, don ceto Najeriya.

“Aiki ne wanda dole ne mu yi shi domin girman Allah da daukakarsa shi kadai.

"Allah yana tare damu, mun yanke shawara a matsayinmu na shugabanni, don samar da wannan tsarin na samun nasarar shugabancin PDP a wannan kasar, a shekarar 2023."

Tambuwal ya bukaci 'yan Najeriya su saka kasa a addu'a don magance matsalar tsaro

Jaridar Today ta lura cewa gwamnan ya bukaci dukkan ‘yan kasa, musamman shugabannin addinai, da su ci gaba da yi wa kasar nan addu’a, musamman kan yanayin tsaro a kasar.

“Muna bukatar addu’a. Allah yana tare da jama’arsa ko yaushe kuma ba zai gajiya da Najeriya ba don daukakarsa,” gwamnan ya kara da cewa.

KU KARANTA: Manya Na Ku Daban: Mutumin da Ya Fi Kowa Iyalai a Duniya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya tabbatar da tsige Cif Letep Dabang a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar, Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a daren Asabar yayin wata liyafar cin abincin dare da aka shirya ta masu ruwa da tsaki a matsayin wani bangare na ayyukan bikin ranar Dimokiradiyya ta 12 ga Yuni wanda aka gudanar a gidan Gwamnatin Rayfield da ke Jos.

Lalong a jawabinsa ya gabatar da sabon Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar in da yake cewa:

“Muna da sabon shugaban jam'iyyar APC a Filato. Yana nan tare da mu. Na gan shi yana kokarin aika sakon tes ta hanyar amfani da wayarsa na ce, bari na tsaya a nan na gabatar dashi kafin ya bace mani.”

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel