Rundunar Yan Sanda Ta Yi Magana Kan Barazanar Wata Ƙungiyar Fulani Na Kai Hari Jihar Delta

Rundunar Yan Sanda Ta Yi Magana Kan Barazanar Wata Ƙungiyar Fulani Na Kai Hari Jihar Delta

  • Rundunar yan sandan jihar Delta, ta yi kira ga mutanen jihar su yi watsi da duk wata barazana da ake yaɗawa
  • Kwamishinan jihar, Muhammed Ari, yace hukumarsa a shirye take ta sauke nauyin dake kanta na kare al'umma
  • Wata ƙungiyar fulani ta yi barazanar kai hari Asaba da kuma Agbor sabida dokar haka fulani kiwo

Biyo bayan barazanar da wata ƙungiyar Fulani mai iƙirarin jihadi ta yi na kai hari Asaba da kuma Agbor na jihar Delta.

Kwamishinan yan sandan jihar, Mr Ari Mohammed Ali, ya sha alwashin bada cikakken tsaro ga al'ummar yankunan, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ka Shirya Wa Kawo Hari Jiharka, Wata Ƙungiya Tayi Wa Gwamna Barazana Saboda Hana Kiwo

Barazanar kai hari jihar Delta
Rundunar Yan Sanda Ta Yi Magana Kan Barazanar Wata Ƙungiyar Fulani Na Kai Hari Jihar Delta Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A wani jawabi da kakakin hukumar yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya fitar, yace:

"An jawo hankalim hukumar mu kan wani rahoto dake yawo, wanda wasu yan fulani dake ikirarin jihadi suka fitar mai taken 'Gargaɗin fulani yan jihadi,' sannan kuma aka liƙa shi a wurare da dama musamman Asaba da Agbor."

"Hukumar yan sanda ƙarƙashin jagorancin, CP Ari Muhammed Ali, a shirye take domin sauke nauyin dake kanta na tabbatar da tsaro ga mazauna jihar Delta."

"Muna kira ga al'umma da su yi watsi da wannan barazanar da ake yaɗawa, wacce wasu bara gurbi suka buga ta domin su saka tsoro tsakanin mutane."

Rundunar yan sandan ta kara da cewa ta yi dukkan wasu shirye-shirye da ya kamata domin daƙile duk wani abu da ka iya faruwa.

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Tabbatar da Mutuwar Mutum 10 a Jihar Plateau

Sannan hukumar ta shawarci mutanen jihar da su cigaba da gudanar da rayuwar su ta yau da kullum kamar yadda suka saba ba tare da tsoro ko tashin hankali ba.

Legit.ng hausa ta gano cewa wata ƙungiyar fulani da ba'a santa ba tayi barazanar kai hari Delta kan dokar hana makiyaya kiyo a fili.

Ƙungiyar tace zata kai hari babban birnin jihar kan nuna goyon bayan dokar hana kiwo da gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa, yayi, kamar yadda punch ta ruwaito.

A wani labarin kuma Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ganduje Ya Taka Hoton Kwankwaso

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa bada sanin gwamna Ganduje ya taka hoton kwankwaso ba.

Kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel