Ka Shirya Wa Kawo Hari Jiharka, Wata Ƙungiya Tayi Wa Gwamna Barazana Saboda Hana Kiwo

Ka Shirya Wa Kawo Hari Jiharka, Wata Ƙungiya Tayi Wa Gwamna Barazana Saboda Hana Kiwo

  • Wata ƙungiya da ba'a santa ba tayi watsi da dokar hana makiyaya kiyo a fili a kudancin ƙasar nan
  • Ƙungiyar ta bayyana matakin da zata ɗauka matuƙar gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, ya cigaba da goyon bayan wannan dokar
  • A wani taro da gwamnonin kudu sukayi, sun amince da kafa dokar hana kiwo a fili a yankunan su

An shiga yanayin tsoro da tashin hankali a jihar Delta bisa barazanar da wata ƙungiya tayi cewa zata kai hari babban birnin jihar kan nuna goyon bayan dokar hana kiwo da gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa, yayi.

KARANTA ANAN: Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayyana Dalilim da Yasa Ganduje Ya Taka Hoton Kwankwaso

Jaridar punch ta ruwaito cewa, ƙungiyar tayi barazanar ne a wata takarda da babu sanya hannun kowa a ciki, wacce aka yi wa take da "Gargaɗin yan jihadin Fulani: buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga jihar Delta," kuma takardar na ɗauke da kwanan watan 13 ga Yuni.

Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa
Ka Shirya Wa Kawo Hari Jiharka, Wata Ƙungiya Tayi Wa Gwamna Barazana Saboda Hana Kiwo Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Takardar wacce aka liƙa ta a wasu sassan jihar ranar Lahadi 13 ga watan Yuni, ta yi gargaɗin cewa za'a kawo hari Asaba da Agbor, jihar Delta, matuƙar gwamna ya gaza cika musu buƙatunsu nan da awanni 72.

Ƙungiyar tace:

"Muna buƙatar gwamnan Delta ya gaggauta canza matsayar da ya ɗauka kan hana makiyaya kiwo a fili wanda jihohi 17 suka amince, cikin awanni 72 daga ranar da aka rubuta wannan wasikar."

"Sannan kuma ya jiye matsayinsa na mai magana da yawun gwamnonin da suka amince da wannan dokar nan take."

KARANTA ANAN: Rundunar Soji Ta Buƙaci Ragowar Yan Boko Haram Su Miƙa Kansu Cikin Ruwan Sanyi

Rahoton vanguard ya nuna cewa, ƙungiyar ta kira yi gwamnan da ya guje wa abun da zai biyo baya idan ya cigaba da goyon bayan hana kiwo a fili.

Ƙungiyar tace:

"Matuƙar aka gaza cika mana buƙatun mu, Jihar Delta, zata faɗa matsanancin yanayi fiye da jihohin Borno, Katsina, Kaduna, Enugu, Benuwai, Oyo, Kebbi da sauran su waɗanda suka ƙi girmama al'adun Fulani."

Hakanan kuma, ƙungiyar ta bayyana cewa tana sane da duk abubuwan dake faruwa a kudancin ƙasar nan, harda wanda aka yi a taron gwamnonin yankin kudu-kudu, kudu-gabas, da Kudu-yamma a Asaba, babban birnin Delta.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗan Sanda a Wani Gumurzu da Suka Yi a Akwa Ibom

Wasu yan bindiga da ake zargin yan ƙungiyar taware IPOB ne sun hallaka ɗan sanda a Akwa Ibom.

Maharan sun buɗe wuta akan ofishin yan sanda dake ƙaramar hukumar Ini, inda aka yi gumurzu a tsakanin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel