Rundunar Soji Ta Buƙaci Ragowar Yan Boko Haram Su Miƙa Kansu Cikin Ruwan Sanyi

Rundunar Soji Ta Buƙaci Ragowar Yan Boko Haram Su Miƙa Kansu Cikin Ruwan Sanyi

  • Sojoji sun yi kira ga ragowar yan ta'addan Boko Haram da su aje makamansu, su rungumi zaman lafiya
  • GOC na runduna ta 7, A. A Eyitayo, shine yayi wannan kiran a wani taron yan jarida da sojoji suka shirya a Maiduguri
  • A halin yanzun yan ta'addan na cikin wani hali saboda ruwan wuta da suke sha daga jami'an soji

Rundunar sojin ƙasa ta yi kira ga ragowar mayaƙan Boko Haram da su miƙa kansu, su rungumi zaman lafiya, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Brig.-Gen. A. A. Eyitayo, GOC na rundunar soji ta 7, shine yayi wannan kira a wani taro da aka shirya wa yan jarida ranar Lahadi a Maiduguri, kamar yadda the cable ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Sokoto-Gusau, Sun Kashe Aƙalla Mutum 12

Mr. Eyitayo, wanda shine kwamandan rundunar Operation haɗin kai, yace matsin lamba da sojoji suke yi akan mayaƙan Boko Haram ɗin yasa ragowar suka fara watsewa.

Rundunar Sojin Ƙasa ta buƙaci yan ta'addan Boko Haram su aje makamansu
Rundunar Soji Ta Buƙaci Ragowar Yan Boko Haram Su Miƙa Kansu Cikin Ruwan Sanyi Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa babu wanda yake son a cigaba da zubar da jini, saboda haka akwai buƙatar ragowar yan ta'addan su rungumi zaman lafiya, su tuba daga ayyukan ta'addanci.

Yace yan Boko Haram su yi amfani da damar da suke da ita su aje makamansu, sannan su rungumi zaman lafiya ta yadda zasu koma rayuwa kamar kowa.

Eyitayo ya yaba da irin gudummuwar da yan jarida suke bayarwa wajen yaƙi da yan ta'adda, ya kuma roƙe su da su watsa wannan sakon ta yadda zai kai ga kunnuwan yan ta'addan.

KARANTA ANAN: Cece-Kuce Yayin da Gwamna Ganduje Yasa Ƙafa Ya Take Hoton Madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso

Yace: "Ba munzo nan domin a cigaba da zubar da jini bane, babu wanda yake jin daɗi mutane na mutuwa."

"Wasu daga cikinsu (yan ta'addan Boko Haram) suna sauraron kafafen watsa labarai, saboda haka yana da kyau mu yi amfani da kafar watsa labarai wajen kira gare su, su aje makamansu, su nemi yafiya da sulhu."

A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Masu Garkuwa 5 a Abuja, Ta Ƙwato Maƙudan Ƙuɗi a Hannunsu

Jami'an yan sanda sun cafke wasu mutum 5 da zargin suna da hannu a satar mutane a Abuja.

Hakanan kuma jami'an sun kwato maƙudan kuɗaɗe a hannun waɗanda suka kama ɗin tare da wasu kayan aikin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel