Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ganduje Ya Taka Hoton Kwankwaso

Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ganduje Ya Taka Hoton Kwankwaso

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa bada sanin gwamna Ganduje ya taka hoton kwankwaso ba
  • Kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Kano
  • Yace kowa yasan gwamna Ganduje da ƙaunar zaman lafiya da girmama mutane, ba zai taba yin haka da gan-gan ba.

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa taka hoton kwankwaso da gwamna Ganduje yayi ba dagangan bane kuma ba shiryayyen abu bane, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, shine ya faɗi haka, yace hoton da ake yaɗawa na gwamna Ganduje yana taka Fastar kwankwaso a wajen taron APC da ya gudana ranar Asabar, amma ba da sanin mai girma gwamna hakan ta faru ba.

KARANTA ANAN: Cece-Kuce Yayin da Gwamna Ganduje Yasa Ƙafa Ya Take Hoton Madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso

Kwamishinan ya ƙara da cewa kowane irin banbancin siyasa ke tsakanin mutanen biyu, ba halayyar gwamna Ganduje bane yayi irin wannan abun ga wani ɗan siyasa, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano
Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayyana Dalilim da Yasa Ganduje Ya Taka Hoton Kwankwaso
Asali: UGC

Yace yayin da ake cigaba da yaɗa hotunan, har wasu sun fara sukar gwamna akan lamarin saboda wata manufar su ta siyasa, lamarin zai iya zama wata babbar matsala idan ba'a fito an bayyana gaskiya ba.

KARANTA ANAN: Murna Ta Koma Ciki: Yadda Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefa Bam a Wurin Taron Ɗaura Aure a Jihar Neja

Da yake bayyana ainihin abinda ya faru, kwamishinan yace:

"A lokacin taron, dandazon mabiya ɗariƙar kwankwasiyya suka sauya sheƙa zuwa APC, lokacin da aka kira gwamna yazo yayi jawabi sai waɗannan tsoffin yan kwankwasiyya suka yi layi a hanyar gwamnan domin nuna goyon bayan su ga gwamnan."

"Wasu daga cikinsu suka fara watsi da hotunan tsohon gwamnan, ɗaya daga cikin hotunan ya faɗo kan kafet din da gwamna zai taka ya wuce, ba tare da sanin Ganduje ba ya taka ya wuce."

Malam Garba yace kowa yasan gwamna Ganduje da son zaman lafiya da girmama mutane, bai kamata ace ana sukar sa kan abinda yayi bada saninsa ba.

A wani labarin kuma Maganar Sulhu Ta Ƙare, Zamu Ɗauki Matakin da Yan Bindiga Suka Fi Gane Wa, Matawalle

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, yace zai ɗauki matakin da ya dace a kan yan bindigan da suka addabi mutane

Gwamnan ya bayyana cewa da farko ya ɗauki matakin sulhu kuma an samu nasara, amma yanzun za'a musu abinda suke so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel