Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗan Sanda a Wani Gumurzu da Suka Yi a Akwa Ibom
- Wasu yan bindiga da ake zargin yan ƙungiyar taware IPOB ne sun hallaka ɗan sanda a Akwa Ibom
- Maharan sun buɗe wuta akan ofishin yan sanda dake ƙaramar hukumar Ini, inda aka yi gumurzu a tsakanin su
- Kakakin hukumar yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin, yace an kashe jami'i ɗaya yayin artabun
Wasu yan bindiga da ake zargin yan ƙungiyar taware ne IPOB, sun kai hari ofishin yan sanda dake ƙaramar hukumar Ini, jihar Akwa Ibom, inda suka hallaka ɗan sanda, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Masu Garkuwa 5 a Abuja, Ta Ƙwato Maƙudan Ƙuɗi a Hannunsu
Rahotan the nation ya bayyana cewa ɗan sandan ya rasa ransa ne yayin musayar wuta da yan bindigan wanda aka jima ana yi.
Wata majiya daga yankin da abun ya faru, ta bayyana cewa an cafke ɗaya daga cikin maharan mai suna, Imo John Udo, yayin da sauran suka tsere da harbin bindiga a jikinsu.
Majiyar ta ƙara da cewa da yawan yan bindigan sun bar abun hawan su tare da zubar da makaman su, sannan suka tsere daga wurin fafatawar.
Majiyar tace: "Wasu yan bindiga akan mashin sun kai hari Ofishin yan sanda dake ƙaramar hukumar Ini, suna isa wurin suka buɗe wa jami'an tsaron wuta, suma suka maida martani, a wannan yanayi aka harbi ɗaya daga cikin yan sandan."
"Yan bindigan sun tsere zuwa cikin daji yayin da suka bar abun hawan su da kuma makaman su a wurin fafatawar."
KARANTA ANAN: Cece-Kuce Yayin da Gwamna Ganduje Yasa Ƙafa Ya Take Hoton Madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Odiko MacDon, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace kwamishinan yan sandan jihar, Mr. Andrew Amiengheme, ya umarci jami'ai su tabbatar da tsaro a yankin sannan su kamo waɗanda suka kawo harin.
A wani labarin kuma Murna Ta Koma Ciki, Yadda Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefa Bam a Wurin Taron Ɗaura Aure a Jihar Neja
Jirgin yaƙin rundunar sojin sama yayi kuskuren jefa bam a kan wasu mutane dake taron murnar ɗaura aure, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da hakan, yace mazauna yankin biyu sun rasa rayuwarsu.
Asali: Legit.ng