Cece-Kuce Yayin da Gwamna Ganduje Yasa Ƙafa Ya Take Hoton Madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso

Cece-Kuce Yayin da Gwamna Ganduje Yasa Ƙafa Ya Take Hoton Madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso

  • Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya fara shan suka kan taka hoton tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso
  • An gano Ganduje na Taka hoton kwankwaso a wurin taron gangami da APC ta gudanar a jihar ranar 12 ga Yuni
  • A halin yanzun har masoyan Ganduje sun fara sukarsa, a cewar su wannan ba dai-dai bane

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, ya fara shan suka kan taka hoton wanda ya gada kuma madugun kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso lokacin taron APC, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Da yake jagorantar gangamin ranar demokaraɗiyya 12 ga watan Yuni, inda ya karbi wasu da suka sauya sheƙa zuwa APC a filin wasan Kano Pillars, gwamna Ganduje ya sa ƙafa ya take hoton kwankwaso.

KARANTA ANAN: Murna Ta Koma Ciki: Yadda Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefa Bam a Wurin Taron Ɗaura Aure a Jihar Neja

Amma gwamnan yana shan suka daga wurin al'umma tako ina kan wannan matakin da ya ɗauka na take hoton.

Ganduje ya taka hoton kwankwaso
Cece-Kuce Yayin da Gwamna Ganduje Yasa Ƙafa Ya Take Hoton Madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Daya daga cikin masoyan gwamnan kuma tsohon kwamishin ayyuka na jihar Kano, Mu'azu Magaji, ya nuna cewa abinda gwamnan yayi ba dai-dai bane.

Yace: "A'a mai girma gwamna a'a, duk wanda ya baka wannan shawarar a matsayin adawar siyasa to baisan mecece siyasa da abinda ta ƙunsa ba."

"Kayi hakuri yallabai, amma abinda kayi ba dai-dai bane a matsayinka na yayan mu kuma shugaban mu. Koma dai menene Rabiu Kwankwaso tsohon gwamnan Kano ne, kuma tsohon minista a Najeriya."

"Kayi tunanin yadda zamu ji idan hakan ta faru da kai bayan ka gama mulkin ka kabar ofis ɗin gwamnan Kano."

Wani da ya faɗi ra'ayinsa kan wannan lamarin, Muhammad Jamu, yace:

"Wannan abun kunya ne ace mutum mai daraja kamar Ganduje ya ɗauki wannan a matsayin adawar siyasa, ya taka hoton mai girma shugaban cigaban Ilimi, Rabiu Musa Kwankwaso."

"Wanda shine mutumin da ta sanadinsa ne ka zama a inda kake yanzun. Saƙo na gareka (Ganduje) a bayyane yake, duk abinda kake gani a yanzun wataran zai wuce. Ina addu'a Allah ya kaimu lokacin da waɗanda ke baka irin wannan shawarar zasu koma suna yaƙi da kai."

KARANTA ANAN: Iyalan MKO Abiola Sun Koka Ga Shugaba Buhari, Sun Ce Har Yanzun Basu Amfama da Komai Ba

Wani mai amfani da facebook, Usman Ali Basuguma, yace:

"Har mabiya jam'iyyar APC zasu tabbatar da cewa duk wanda ya bada umarnin aikata haka ba ƙwararre bane, baima san abinda yake ba."

"Ganduje, adawar ka ga kwankwaso ce zata cinye maka lokacinka, ka zama gwamna shekara 6 da ta wuce amma mutumin nan ya fika masoya na haƙiƙa, yan aƙida."

Tosin Anthony Fapohund, yace:

"Ganduje ya taka hoton tsohon uban gidansa, wato siyasa da yan siyasa suna da abun mamaki. Duk wanda ya baiwa gwamna Ganduje wannan shawarar lallai ƙaramin ɗan siyasa ne."

A wani labarin kuma Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Tare da Jiga-Jigan Kwankwasiyya 27 Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Kano

Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano tare da wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan Jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yace sun ɗauki matakin da ya dace kuma a lokacin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel