Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Sokoto-Gusau, Sun Kashe Aƙalla Mutum 12

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Sokoto-Gusau, Sun Kashe Aƙalla Mutum 12

  • Wasu ɗauke da makamai da ake zargin yan bindiga ne sun kashe mutum 12 a garin Maikujera dake jihar Zamfara
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace an kai harin ne da yamma
  • Hakanan wasu yan bindiga sun tare hanyar Sokoto-Gusau, inda suka yi awon gaba da matafiya da dama

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe mutum 12 a Maikujera, ƙaramar hukumar Rabah, jihar Sokoto, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

MARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗan Sanda a Wani Gumurzu da Suka Yi a Akwa Ibom

Da yake tabbatar da kai harin, kakakin rundunar yan sandan jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, yace an kai harin ne ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

A cewar sa, maharan sun samu nasarar kashe mutum 12 a yayin harin, amma basu sace kowa ba.

Yan bindiga sun kashe mutum 12 a Sokoto
Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Sokoto-Gusau, Sun Kashe Aƙalla Mutum 12 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A ranar Lahadi kuma, wasu da ake zargin yan bindiga ne suka tare hanyar Sokoto-Gusau na tsawon awanni.

Wani ɗan Okada, wanda yana cikin waɗanda aka tare a hanyar yace Yan bindigan sun tare hanyar Bimasa-Lambar Bakura, inda suka gudanar da aikin su na tsawon awanni biyu.

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Masu Garkuwa 5 a Abuja, Ta Ƙwato Maƙudan Ƙuɗi a Hannunsu

Legit.ng hausa ta gano cewa yan bindigan sun yi awon gaba da adadi mai yawa na fasinjojin da suka biyo hanyar a wannan lokacin.

A cewar ɗan Okadan: "Da yawan matafiyan dake son bin hanyar dole suka tsaya a Bamasa har sai bayan yan bindigan sun bar wurin."

Kakakin yan sandan, ASP Abubakar, yace ba zai iya tabbatar da lamarin ba saboda ya faru ne a yankin jihar Zamfara.

A wani labarin kuma Cece-Kuce Yayin da Gwamna Ganduje Yasa Ƙafa Ya Take Hoton Madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya fara shan suka kan taka hoton tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

An gano Ganduje na Taka hoton kwankwaso a wurin taron gangami da APC ta gudanar a jihar ranar 12 ga Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel