Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Masu Garkuwa 5 a Abuja, Ta Ƙwato Maƙudan Ƙuɗi a Hannunsu

Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Masu Garkuwa 5 a Abuja, Ta Ƙwato Maƙudan Ƙuɗi a Hannunsu

  • Jami'an yan sanda sun cafke wasu mutum 5 da zargin suna da hannu a satar mutane a Abuja
  • Hakanan kuma jami'an sun kwato maƙudan kuɗaɗe a hannun waɗanda suka kama ɗin tare da wasu kayan aikin su
  • Kakakin hukumar yan sandan Abuja, ASP Yusuf Mariam, tace za'a kai mutanen kotu da zaran an kammala bincike

Rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta cafke mutum 5 da zargin masu garkuwa da mutane ne a Tungan-maje, Bwari da Kwali-Kuje, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Cece-Kuce Yayin da Gwamna Ganduje Yasa Ƙafa Ya Take Hoton Madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso

Kakakin yan sandan, ASP Yusuf Mariam, ita ce ta bayyana haka a wani jawabi da ta fitar, ta bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da; Usman Musa, Bello Musa, da Haruna Alhassan.

Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Masu Garkuwa 5 a Abuja, Ta Ƙwato Maƙudan Ƙuɗi a Hannunsu
Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Masu Garkuwa 5 a Abuja, Ta Ƙwato Maƙudan Ƙuɗi a Hannunsu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Tace jami'an yan sanda dake yaƙi da masu garkuwa da mutane sune suka samu nasarar cafke waɗanda ake zargin a wani aiki da suka fita bayan samun rahoton sirri.

ASP Mariam tace: "Waɗanda aka kama ɗin suna da alaƙa da wata tawagar masu garkuwa da mutane, kuma sun amsa laifin su. Sun ce suna da hannu a sace-sacen mutanen yankin Bwari-Byzahin, Kuje-Kwali da kuma jihar Neja."

"Jami'ai sun kwato kuɗi kimanin Naira miliyan N1,270,000 da aka basu kuɗin fansa, wayoyin hannu guda uku, agogon hannu 3, da hula guda 2."

KARANTA ANAN: Murna Ta Koma Ciki: Yadda Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefa Bam a Wurin Taron Ɗaura Aure a Jihar Neja

"Sannan jami'an mu sun damƙe wasu mutum biyu, Lawal Abdullahi, da Abdul Alhassan, dake da hannu a satar mutane a yankin Tungan Maje."

Mrs. Yusuf ta ƙara da cewa da zaran an kammala bincike za'a gurfanar da waɗanda ake zargin gaban kotu.

A wani labarin kuma Iyalan MKO Abiola Sun Koka Ga Shugaba Buhari, Sun Ce Har Yanzun Basu Amfama da Komai Ba

Iyalan Marigayi MKO Abiola sun nuna damuwarsu kan yadda gwamnatin tarayya tayi watsi da su, kamar yadda punch ta ruwaito.

A cewar iyalan marigayin wanda ya lashe zaɓen June 12, har yanzun gwamnati ta kasa cika alƙawurran da ta yi musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel