Kaduna: Bayan Harin Kwalejin Nuhu Bamalli, Ƴan Bindiga Sun Yi Yunƙurin Kai Hari Wata Makarantar Sakandare
- Awanni kadan bayan harin da aka kai Kwalejin Nuhu Bamalli a Zaria, yan bindiga sunyi yunkurin kai hari makarantar sakandare a Kujama
- Sai dai jaruman jami'an tsaro a Kaduna sun dakile harin sun fatattaki ƴan bindigan
- Ƴan bindiga sun sauya shirin su sun tare wasu matafiya sun yi awon gaba da wasu amma daga bisani an ceto su
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce jami'an tsaro sun dakile wata hari da yan bindiga suka yi yunkurin kai makarantar sakandare ta Prelude College da ke Kujama, ƙaramar hukumar Chikun, rahoton The Cable.
Vanguard ta ta ruwaito cewa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a.
DUBA WANNAN: Kowa ya kare kansa daga 'Yan Bindiga: Matawalle ya faɗawa Zamfarawa
Hakan na zuwa ne awanni bayan harin da yan bindiga suka kai Kwalejin Nuhu Bamalli a jihar inda suke sace mutum 10 tare da halaka ɗalibi ɗaya.
Aruwan ya ce yan bindigan sun kai wa wasu matafiya hari a hanyar Kaduna zuwa Kachia inda mutum uku suka jikkata.
Ya ce an ceto mutum biyun da suka sace.
Kazalika, Aruwan ya ce jami'an tsaron sun dakile harin da aka kai a hanyar Zaria zuwa Kano a ƙaramar hukumar Makarfi.
KU KARANTA: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi
"Jami'an tsaron da aka tura yankin sun halaka wani ɗan bindiga sanye da kayan sojoji sun kuma kwato bindiga ɗaya," in ji kwamishinan.
Ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya jinjina wa jami'an tsaron ya kuma yi addu'ar Allah ya jikan wanda ya rasu tare da fatan samun sauki ga wanda ya jikkata.
A wani rahoton daban, kun ji cewa mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami'ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.
Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.
Asali: Legit.ng