Manya Na Ku Daban: Mutumin da Ya Fi Kowa Iyalai a Duniya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Manya Na Ku Daban: Mutumin da Ya Fi Kowa Iyalai a Duniya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Wani mutumin da aka ce shine yafi kowa iyalai a duniya ya mutu bayan wata 'yar karamar jinya
  • Rahotanni sun bayyana yadda adadin iyalansa da kumaa irin gudunmawarsa ga jiharsa a Indiya
  • Babban ministan jihar ya mika ta'aziyyarsa, ya kuma bayyana matsayin iyalin mutumin a yankin

Wani mutum a arewa maso gabashin Indiya, wanda ya fi kowa yawan iyali a duniya, ya mutu.

Ziona Chana mai shekaru 76. Iyalinsa sun ce ya yi fama da ciwon suga da hawan jini wanda ya yi sandiyyar mutuwarsa, BBC ta ruwaito.

Mista Chana yana da mata 39 da yara 94 da kuma jikoki da yawa.

KU KARANTA: Zagon Kasa: An Kori Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Filato an Nada Mataimakinsa

Manya na ku daban: Mutumin da ya fi kowa iyalai a duniya a riga mu gidan gaskiya
Iyalan Ziona Chana dake kasar Indiya | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Ya zauna tare da dukkanin iyalinsa a wani gidan bene hawa hudu da ke wani kauye mai tsaunuka a jihar Mizoram, da ke iyaka da kasar Myanmar a yankin Asiya.

Jami'ai sun ce gidan ya zama wani babban wurin jan hankali ga 'yan yawon bude ido saboda yawan iyalin mutumin.

Mista Chana ya shugabancin wata kungiyar mabiya addinin Kirista da ke da'awar ba da damar auren mata fiye da daya. Ya fara yin aure yana da shekara 17.

Babban Ministan Mizoram Zoramthanga ya yi wa iyalansa ta’aziyya kuma ya ce dangin su ne babban wurin jan hankalin ‘yan yawon bude ido a jihar, India Tv News ta ruwaito.

KU KARANTA: Ganduje: Zan Yi Maganin Duk Dan Siyasar da Ke Son Bata Siyasarmu Da ’Yan Daba

A wani labarin, Elisane Silva, duk da cewa ba a hukumance ba, amma itace mace mafi tsayi a kasar Brazil, in ji rahoton Daily Mail.

Budurwar da ta fito daga Salinopilis a kasar Brazil ta fara lura da saurin girmanta lokacin tana da shekaru 10.

A baya tsawonta yakai kafa 5 da inci 9 to amma a yanzu ta kai kafa 6 da inci 8.

Budurwar mai shekaru 26 ta ce ta sha wahala ta fuskar zagi da izgili saboda tsayinta kuma sau da yawa takan kulle kanta domin ta nisanci jama'a, Metro.co.uk ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.