Abun Ban Sha’awa: Hotunan Yarinyar da Ta Fi Kowa Tsawo a Brazil Tare da Mijinta

Abun Ban Sha’awa: Hotunan Yarinyar da Ta Fi Kowa Tsawo a Brazil Tare da Mijinta

  • A wani sanannen labari, wata budurwa mai shekaru 26 ta auri wani mutum mai shekaru 31
  • Ba abun mamaki bane auren, sai dai, tsawonsu ya sha bam-bam, domin ta dara shi da kafa 2
  • Rahotanni sun bayyana yadda suka hadu, suka yi aure duk da cewa ita mai tsawo ce sama da shi

Elisane Silva, duk da cewa ba a hukumance ba, amma itace mace mafi tsayi a kasar Brazil, in ji rahoton Daily Mail.

Budurwar da ta fito daga Salinopilis a kasar Brazil ta fara lura da saurin girmanta lokacin tana da shekaru 10.

A baya tsawonta yakai kafa 5 da inci 9 to amma a yanzu ta kai kafa 6 da inci 8.

KU KARANTA: Ganduje: Zan Yi Maganin Duk Dan Siyasar da Ke Son Bata Siyasarmu Da ’Yan Daba

Yarinyar da ta fi kowa tsawo a Brazil ta yi wuff da matashin da ta dara tsawo nesa
Yarinyar da ta fi kowa tsawo a kasar Brazil tare da mijinta da yaronsu Hoto: dailymail.com
Asali: UGC

Budurwar mai shekaru 26 ta ce ta sha wahala ta fuskar zagi da izgili saboda tsayinta kuma sau da yawa takan kulle kanta domin ta nisanci jama'a, Metro.co.uk ta ruwaito.

Yadda ta fara soyayya da wani dan shekaru 31

Elisa daga baya ta yi aurenta tare da wani mutumi mai suna Francinaldo Da Silva Carvalho a cikin shekarar 2015.

A cewarta, sun hadu ne a shekarar 2011 kuma sun fada tsananin soyayya da kaunar juna. Gamayyar ta yi kyau, domin kuwa sun samu karuwar da.

Elisa ta yaba da gaskiyar cewa mijinta na son ta duk da bambancin tsawonsu kuma bai taba ganin hakan a matsayin matsala ba.

Ta ce:

"Na ji wata alaka nan take a lokacin da na hadu da shi, kuma ban ma lura da tsayinsa ba.
"Tsawon Francinaldo bai wuce kafa 5 da inci 4, wanda na dara shi da kafa kusan biyu - amma ban damu ba.
"Duk da cewa yana sane da tsayina da yanayina, bai yi wata munanan maganganu ba, kuma bai taba nuna damuwa ba."

KU KARANTA: Zagon Kasa: An Kori Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Filato an Nada Mataimakinsa

A wani labarin, Wata sanarwa da wata mai magana da yawun gwamnati, Phumla Williams ta yi kwanan nan, ta bayyana cewa gwamnati ba ta da wata shaida da ke nuna cewa wata mata Gauteng mai suna Gosiame Thamara Sithole ta haifi jarirai 10 a lokaci guda.

"Gwamnati ta kasa tantance sahihancin waccar haihuwar a cibiyoyinmu," in ji wani bangare na sanarwar da Williams ta fitar.

Tun da farko an samu shakku game da labarin haihuwar mai ban mamaki na wata matar da aka ce ta haifi jarirai 10 a kasar Afrika ta Kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel