Jinkirta Sallar Asuba ya sa Sheikh Sudais ya tube shugaban limamai a Saudiyya

Jinkirta Sallar Asuba ya sa Sheikh Sudais ya tube shugaban limamai a Saudiyya

- Sheikh Sudais, shugaban Masallatan Haramain Sharifaini ya tuntubuke shugaban limaman masallacin Madina

- Rahoton masallatan biyu ya bayyana cewa, an dakatar da shugaban ne saboda jinkirta sallah da aka yi a masallaci

- Sheikh Sudais ya bayyana sabon tsarin yadda za a ke gabatar da sallah a masallacin bayan faruwar lamarin

Shugaban Masallatai biyu mafi daraja a Saudiyya (Haramain Sharifain) Sheikh Abdul Rahman Al Sudais ya tube Daraktan da ke kula da limamai da ladanai a masallacin Manzon Allah dake birnin Madina.

An tube shi ne saboda samun jinkirin tayar da sallar Asuba bayan an kira Sallah na tsawon minti 45, kamar yadda Hukumomin da ke kula da Masallatan Makkah da Madina a Saudiyya, Haramain Sharifain suka sanar.

Sanarwar da aka wallafa a Facebook ta ce shugaban Masallatan Sheikh Abdul Rahman Al Sudais ya bukaci a samar da limamai biyu a ko wace Sallar farilla tare da ladanai uku masu jiran ko ta kwana.

KU KARANTA: Da dumi: dumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure 3 a jihar Kaduna

Jinkirta Sallar Asuba ya sa Sheikh Sudais ya tube shugaban limamai a Saudiyya
Jinkirta Sallar Asuba ya sa Sheikh Sudais ya tube shugaban limamai a Saudiyya Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Sanarwar ta karanta:

Sakamakon jinkirin da aka samu a sallar Asuba a yau sama da mintuna 45 tsakanin kiran sallah da Iqaamah, sai aka cire daraktan sashen na Limamai da Ladanai daga matsayinsa.
Nan gaba, ga kowace Sallah, za'a sami Limamin da aka sanya tare da Na'ibinsa, Ladanai 3 da aka warewa kowace sallah. Ladan daya yana kiran sallah daya na kiran Iqaamah da mataimaki daya.

KU KARANTA: Ku taimaka ku ceci Najeriya: NCF ta roki Gowon, sauran tsoffin shugabanni

A wani labarin, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da dawo da kwamishinoni uku da shugabannin hukuma uku na hukumomin jihar.

The Guardian ta ruwaito cewa a ranar 1 ga Yuni, Matawalle ya kori Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) Alhaji Bala Bello da dukkan kwamishinoninsa 23 nan take.

Dawo dasu aikin na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Alhaji Kabiru Balarabe, shugaban ma’aikatan jihar kuma mukaddashin sakataren gwamnatin jihar a Gusau ranar Talata, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel