Ba alluran Korona ke damuna na, sanya takunkumin fuska ke damuna, Shugaba Buhari

Ba alluran Korona ke damuna na, sanya takunkumin fuska ke damuna, Shugaba Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda yake ji bayan yin allurar rigakafin Korona
  • Shugaban ya kuma ce, amfani da takunkumin fuska na matukar damunsa sabanin rigakafin da ya yi
  • Shugaban ya yi allaran rigakafin a a karon farko cikin watan Maris da kuma Mayu a karo na biyu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu abinda ke damun sa bayan da aka yi masa allurar rigakafin Korona karo na biyu sai dai saka takunkumin kariya daga cutar, BBC ta ruwaito.

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi da gidan na NTA a daren jiya Juma'a 11 ga watan Yuni, 2021.

Yayin da dan jarida Adamu Sambo ya tambaye shi: "Kwana nan aka yi maka rigakafin korona karo na biyu, ko akwai wani abu da allurar ta haddasa maka?"

KU KARANTA: Ku daina jira sai na zo na magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari ga gwamnoni

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana game da ra'ayinsa kan sanya takunkumin fuska
Shugaban kasar Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari (Mai Ritaya) sanye da takunkumin fuska Hoto: humangle.ng
Asali: UGC

Sai shugaba Buhari ya amsa da cewa: "Babu wani abu da nake ji zuwa yanzu. Amma saka wannan abin da na ake kira da takunkumi yana damu na gaskiya."

Bayan sanya dokar hukunta masu karya dokar sanya takunkumi, Buhari ya karya dokar

Cikin wasu hotuna da suka yadu a kafafen sada zumunta, an ga shugaba Buhari yana magana da wasu jiga-jigan siyasa na jam'iyyar APC ba tare da takunkumi a fuskarsa ba.

Shugaban shi ne ya sanya dokar hukunta duk wanda ya shiga bainar jama'a ba tare da takunkumin fuska ba, lamarin ya da ya jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya, Punch ta ruwaito.

An yi wa Shugaba Buhari allurar rigakafin Korona

A watan mayu ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi allurar rigakafin Korona ta Oxford-AstraZeneca kashi na biyu a gidan gwamnati dake Abuja.

A baya an ruwaito cewa likitan shugaban kasar na musamman, Suhayb Rafidadi ne ya yi wa shugaban rigakafin a gidansa da ke fadar gwamnati, Abuja ranar Asabar 29 ga watan Mayu.

Shugaba Buhari ya karbi rigakafin kashi na farko a ranar 6 ga watan Maris inda jami’an Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya suka gabatar masa da katin shaidar karbar rigakafin Korona.

Shugaban, da sauran manyan mukarraban gwamnati a Najeriya sun karbi allurar rigakafin annobar Korona, kuma an yi dubban 'yan Najeriya allurar kawo yanzu.

Shugaban Buhar i shine zakaran ECOWAS akan Yaki da annobar Korona, Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA: Yadda 'yan sanda suka kame masu hada wa 'yan ta'addan IPOB guruye da layu

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, ya bayyana cewa makiyaya a Najeriya basa daukar komai sama da sanduna da adda don tara ciyawar shanun su.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa shugaban a tattaunawarsa da 'yan jaridu a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV ya dage cewa makiyaya 'yan asalin Najeriya basa amfani da manyan makamai kamar AK-47.

Da yake ci gaba da magana, shugaban na Najeriya ya bayyana makiyayan da ke dauke da muggan makamai cewa ba 'yan Najeriya bane, tabbas daga wasu kasashen suke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel