Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Cafke Wani Riƙakken Ɗan Leƙen Asirin ISWAP a Borno

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Cafke Wani Riƙakken Ɗan Leƙen Asirin ISWAP a Borno

  • Jami'an soji a jihar Borno sun cafke wani sanannen ɗan leƙen asirin ƙungiyar ISWAP
  • Mutumin mai suna Goni Faidam, ya kasance yana sanar da yan ta'addan shirin jami'an soji da kuma motsin su
  • A cewar wata majiya daga cikin jami'an soji, wanda aka kama ɗin yana da albashin N250,000 duk wata

Jami'an rundunar sojin ƙasa sun cafke wani sanannen ɗan leƙen asirin ƙungiyar ISWAP, wanda yake ɗaukar bayanan jami'an tsaro yana kaiwa kwamandojin ƙungiyar, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 60 a Jihar Zamfara

Wani jami'i a ɓangaren fasaha na rundunar ya shaida wa PRNigeria cewa wanda ake zargin mai suna, Goni Fandam, ya kasance a koda yaushe aikinsa shine binciko shirin jami'an tsaro ya sanar da yan ta'adda.

Jami'an rundunar sojin ƙasa
Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Cafke Wani Riƙakken Ɗan Leƙen Asirin ISWAP a Borno Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kafin Sojoji su binciko shi kuma su samu nasarar kama shi yana aikin leƙen asirin jami'an soji a Borno.

KARANTA ANAN: An Kashe Wani Ɗalibin Kwalejin Fasaha Mako Ɗaya Kafin Bikin Aurensa a Ibadan

Yace: "Bayan binciko alaƙar sa da manyan kwamandojin ƙungiyar ta'addancin ISWAP, sojoji sun gano inda yake a maɓoyar sa dake Mainok."

"Yana daga cikin yan leƙen asirin da ake biyansu N250,000 duk wata domin su gano shirye-shirye da kuma motsin jami'an soji."

"Ina ƙara tabbatar muku cewa, yana samar wa yan ta'addan bayanai a kan matafiya tsakanin Jakara da Auno da kuma Maiduguri zuwa Damaturu."

Legit.ng hausa ta gano cewa, Manjo DY Chiwar, shine ya jagoranci sojoji suka je har maɓoyar ɗan leƙen asirin suka kamo shi.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sace Jariri Ɗan Shekara 3 Tare da Matan Aure 5 a Abuja

Wasu yan bindiga sun kutsa har cikin gida a Anguwan Epe, sun yi awon gaba da jariri tare da mata 5.

Wani mazaunin yankin, Ishaku, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace maharan sun zo cikin shiri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel