Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 60 a Jihar Zamfara

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 60 a Jihar Zamfara

  • Wasu yan bindiga sun hallaka mutum 60 a wani ƙauye dake ƙaramar hukumar Zurmi, jihar Zamfara
  • Wani shaida ya bayyana cewa mutanen garin sun watse gaba ɗaya domin tsira da rayuwarsu
  • Ya ƙara da cewa an shirya za'a yi wa waɗanda suka mutu jana'iza a fadar Sarkin Zurmi

Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 60 a ƙauyen Kadawa dake ƙaramar hukumar Zurmi, jihar Zamfara, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: An Kashe Wani Ɗalibin Kwalejin Fasaha Mako Ɗaya Kafin Bikin Aurensa a Ibadan

Wani shaida ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Alhamis, inda suka kashe mutum 54.

Yam bindiga sun kashe mutun 60 a Zamfara
Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 60 a Jihar Zamfara Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewarsa, yan bindigan sun yi awon da gaba da shanu da dama, sannan sun shiga shaguna sun ɗebi kayayyaki da yawa.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Sace Jariri Ɗan Shekara 3 Tare da Matan Aure 5 a Abuja

Shaidan yace: "Yan bindigan sun kashe mutum 54 kuma dukkan su maza ne. Babu mutanen da zasu musu jana'iza saboda mazauna garin sun watse."

"A halin yanzun, muna tattara gawarwakinsu ne zamu kai faɗar mai martaba sarkin Zurmi, inda aka shirya za'a yi musu jana'iza baki ɗaya."

Amma wata majiya ta daban ta bayyana cewa yan bindigan sun kashe mutum sama da 60 a harin.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Sheƙe Sufetan Ofishin

Wasu yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda inda suka hallaka sufetan yankin, kamar yadda punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi musayar wuta tsakanin jami'an yan sanda da kuma maharan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262