Da Ɗumi-Ɗumi: Ku Gyara Halinku, Ku Tabbatar da Tsaro a Najeriya Idan Kuna Son Aikin Yi, Buhari ga Matasa

Da Ɗumi-Ɗumi: Ku Gyara Halinku, Ku Tabbatar da Tsaro a Najeriya Idan Kuna Son Aikin Yi, Buhari ga Matasa

- Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ga gargaɗi matasan Najeriya da su gyara halin su idan suna son aikin yi

- Buhari ya faɗi hakane yayin wata fira da yayi da kafar watsa labarai ranar Alhamis da safe

- Yace babu wani mutum da zai so ya zuba hannun jarin sa a wurin da ya tabbatar babu tsaro

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gargaɗi matasan Najeriya su gyara halinsu, su tabbatar da tsaro a ƙasa matuƙar suna son aikin yi a Najeriya.

KARANTA ANAN: An Kashe Mutum 500 Tare da Sace Wasu 201 a Mazaɓar da Nake Wakilta, Ɗan Majalisa

Buhari yace babu wani da zai so zuba hannun jarinsa a ƙasar da babu tsaro, yanayin da acewar shugaban shine yake ƙara durkusar da ƙasar a yanzun, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaba Buhari yayi wannan maganar ne a wata fira da yayi da 'Arise TV' da safiyar Alhamis.

Da Ɗumi-Ɗumi: Ku Gyara Halinku, Ku Tabbatar da Tsaro a Najeriya Idan Kuna Son Aikin Yi, Buhari ga Matasa
Da Ɗumi-Ɗumi: Ku Gyara Halinku, Ku Tabbatar da Tsaro a Najeriya Idan Kuna Son Aikin Yi, Buhari ga Matasa Hoto: @BashirAhmad
Asali: Instagram

Buhari yace: "Na bada umarnin a faɗawa matasa su gyara halinsu, su tabbatar da tsaro a Najeriya sai a samu mutanen da zasu zo su zuba hannun jarinsu. Najeriya tana da ma'adanai sosai, Allah ya zaɓe mu."

Shugaba Buhari ya koka da zanga-zangar EndSars da aka yi wanda wasu bara gurbi suka shiga cikin matasa, yace "Kusan gidaje 200 wasu baragurbin matasa suka ƙona mallakin tsohon gwamnan Lagos. Wa zaije irin wannan wurin ya zuba dukiyarsa? A hankalce babu.".

KARANTA ANAN: FG Ta Kafa Sabbin Sharuɗda 3 Kan Twitter, Facebook da Instagram Ko Ta Hana Amfani da Su

Shugaban ya gargaɗi matasa su zama na ƙwarai idan suna son samun ayyukan yi saboda tsaro shi ke jawo hankalin masu zuba hannun jari.

"Ya kamata matasa su hankalta, sun tabbatar da tsaro a ƙasar su, saboda babu wanda zai zuba dukiyarsa a wurin da ba tsaro." inji Buhari.

A wani labarin kuma Yan Majalisar Wakilai Sun Buƙaci Shugaban Hukumar FIRS Yayi Murabus Daga Muƙaminsa

Kwamitin dake kula da asusun fili na gwamnati a majalisar wakilai ta ƙasa yayi kira ga shugaban FIRS yayi murabus, kamar yadda punch ta ruwaito.

Kwamitin ya nuna matukar damuwarsa bisa ƙin halartar gayyatar da aka masa don ya amsa tambayoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel