Muhimman abubuwa 7 da shugaba Buhari ya fada yayin wata hira a ranar 11 ga Yuni

Muhimman abubuwa 7 da shugaba Buhari ya fada yayin wata hira a ranar 11 ga Yuni

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata hira ta musamman da Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) a ranar Juma’a, 11 ga Yuni, inda ya amsa wasu tambayoyi game da aikin gwamnati da sauran batutuwan da suka shafi kasa.

Legit.ng ta tattaro wasu muhimman abubuwan da shugaban ya fada a jiya yayin hirar kamar haka

  1. 'Yan Najeriya suna da matukar mantuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ‘yan Najeriya na matukar mantawa da nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru shida da suka gabata. A cewar jaridar The Punch, ya kuma ce wadanda ke son sukarsa su yi shi da idon basira

2. Yawancin 'yan Nijeriya suna yaba ni, sun fahimci abin da muke yi

Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa yawancin ‘yan Najeriya suna yaba masa kuma sun fahimci abin da yake yi wa kasar tunda ya hau mulki a cikin shekaru shida da suka gabata.

KU KARANTA: Makiyaya basa rike AK-47, sanduna da adduna kadai suke rikewa, in ji Buhari

Jawaban shugaban kasa ga manema labarai jiya Juma'a
Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

3. Gwamnatin Tarayya bata da wasu guraben aiki

Shugaba Buhari ya ce gwamnatin tarayya ba ta da sauran guraben aiki. Ya yi gargadin cewa idan matasa suka ci gaba da ingiza rashin tsaro, ba za a samu ayyukan yi daga masu saka jari daga kasashen waje ba.

4. Zan ji da 'yan bindiga da yaren da suka fi fahimta

Shugaban ya ce wadanda suke zarginsa da yin sake ga 'yan bindiga da' yan ta'adda a Najeriya ba su masa adalci ba. Ya karyata sakaci ga 'yan fashi da makami yayin da ake zarginsa da kakkausar murya ga masu tayar da kayar baya a kudu maso gabas.

5. Gwamnatina bata aikata mummunan abu ba

Shugaban Buhari ya ce gwamnatinsa ba ta kaza kan abin da ya shafi tsaro da sauran fannonin gudanar da mulki a kasar.

6. Zan kama, kuma in daure wadancan dake kone ofisoshin 'yan sanda, masu haifar da matsala a Najeriya

Buhari ya yi gargadin cewa wadanda ke kona ofisoshin ‘yan sanda da kuma haifar da hargitsi a kasar za a kama su, a gurfanar da su, sannan a tura su gidan yari.

A cewar jaridar Vanguard, ya ce gwamnatinsa ba za ta kyale wadanda ke haifar da rudani a cikin kasar ba.

7. Buhari ya nuna rashin gamsuwa da tattalin arzikin Najeriya

Shugaban ya nuna rashin gamsuwa da yanayin tattalin arzikin Najeriya. Premium Times ta ruwaito cewa ya sake nanata shirin gwamnatinsa na gyara tattalin arziki da samar da dama ga ‘yan Najeriya.

KU KARANTA: Yadda 'yan sanda suka kame masu hada wa 'yan ta'addan IPOB guruye da layu

A wani labarin daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnoni da su daina jiransa don warware duk wata matsala da suke fuskanta, yana mai cewa ya kamata su dakatar da kai hare-haren makiyaya a jihohinsu., Sahara Reporters ta ruwaito.

Jihohi da yawa na fuskantar munanan hare-hare kan al'ummomi, inda ake fama da rikici ta fuskoki da dama ciki har da na makiyaya, wanda yasa ake matsa wa Shugaban kasa a matsayinsa na Babban Kwamandan sojin kasar da ya kawo dauki.

Kasancewarsa Bafulatani, da yawa daga yankunan kudancin Najeriya sun zarge shi da nuna son kai da rashin son magance hare-hare daga makiyaya, wadanda kuma galibi Fulani ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.