Makiyaya basa rike AK-47, sanduna da adduna kadai suke rikewa, in ji Buhari
- Shugabab kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, makiyayan Najeriya basa daukar AK-47
- Shugaban ya ce iyakar abinda Fulani makiyaya 'yan Najeriya ke dauka sune sanduna da adduna
- Ya kuma bayyana amfanin sanda da adda a wajen Fulani makiyaya asalin 'yan Najeriya da yake magana akai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, ya bayyana cewa makiyaya a Najeriya basa daukar komai sama da sanduna da adda don tara ciyawar shanun su.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa shugaban a tattaunawarsa da 'yan jaridu a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV ya dage cewa makiyaya 'yan asalin Najeriya basa amfani da manyan makamai kamar AK-47.
Da yake ci gaba da magana, shugaban na Najeriya ya bayyana makiyayan da ke dauke da muggan makamai cewa ba 'yan Najeriya bane, tabbas daga wasu kasashen suke.
KU KARANTA: Yadda 'yan sanda suka kame masu hada wa 'yan ta'addan IPOB guruye da layu
Ya bayyana cewa Fulani daga kasashen Mauritaniya da Afirka ta Tsakiya suna kama da juna, ya kara da cewa mutane galibi suna yi musu kallon su 'yan Najeriya ne, P.M News ta ruwaito shi yana cewa.
Buhari ya ce:
"Mai kiwon shanu na Najeriya ba zai dauki komai sama da sanda ba… wani lokacin kuma adduna don sare wasu bishiyoyi."
“Amma wadancan gogaggu wadanda suke dauke da AK-47… a duk yankin Sahel, mutane suna garzayowa zuwa Najeriya. Ku sani, Fulani daga Mauritaniya da Afirka ta Tsakiya kamarsu daya. Don haka suna ganin su ‘yan Najeriya ne.”
KU KARANTA: Wata sabuwa: Makiyaya sun sace fasinjoji 15 a jihar Imo
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnoni da su daina jiransa don warware duk wata matsala da suke fuskanta, yana mai cewa ya kamata su dakatar da kai hare-haren makiyaya a jihohinsu., Sahara Reporters ta ruwaito.
Jihohi da yawa na fuskantar munanan hare-hare kan al'ummomi, inda ake fama da rikici ta fuskoki da dama ciki har da na makiyaya, wanda yasa ake matsa wa Shugaban kasa a matsayinsa na Babban Kwamandan sojin kasar da ya kawo dauki.
Kasancewarsa Bafulatani, da yawa daga yankunan kudancin Najeriya sun zarge shi da nuna son kai da rashin son magance hare-hare daga makiyaya, wadanda kuma galibi Fulani ne.
Asali: Legit.ng