An Kashe Wani Ɗalibin Kwalejin Fasaha Mako Ɗaya Kafin Bikin Aurensa a Ibadan
- Wasu yan fashi da makami sun hallaka ɗalibin dake ajin ƙarshe a kwalejin fasaha Ibadan, jihar Oyo
- Rahotanni sun bayyana cewa marigayi Ebenezer Ayeni ya mutu ne saura mako daya a ɗaura mishi aure
- Kakakin kwalejin fasaha ɗake Ibadan ya tabbatar da faruwar lamarin, yace sun yi babban rashi
Wani ɗalibin dake ajin ƙarshe a kwalejin fasaha dake Ibadan, jihar Oyo, ya rasa rayuwarsa mako ɗaya kafin bikin aurensa, kamar yadda the nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Amince da Naɗin Sabon Darakta Janar Na NBC
Ɗalibin mai suna, Ebenezer Ayeni, dake karatun fasahar waƙa a kwalejin ya rasa ransa ne ranar Alhamis da safe a yankin Ojoo, Ibadan, jihar Oyo.
Kakakin yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya tabbatar da kisan ɗalibin ga jaridar dailytrust ranar Jumu'a.
Kakakin kwalejin fasaha dake Ibadan, Alhaji Adewole Soladoye, yace mutuwar wannan ɗalibin babban rashi ne ga makarantar da al'umma baki ɗaya.
Legit.ng hausa ta gano cewa, Ayeni, wanda shine shugaban ɗalibai kiristoci na kwalejin, zai angonce ne mako mai zuwa a Ibadan kafin mutuwarsa.
Da yake jawabin dangane da lamarin, Soladoye, yace marigayi Ayeni yaje ganin mahaifiyarsa ne a Ojoo lokacin da yan fashi da makami suka kai hari yankin.
KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Sace Jariri Ɗan Shekara 3 Tare da Matan Aure 5 a Abuja
Bayam maharan sun gama abinda zasu yi a yankin, sai suka nemi Ayeni ya musu jagora zuwa ƙauyukan dake maƙwabtaka da Ojoo amma yaƙi amincewa shine suka harbesa a kafa.
A cewarsa, an kai Ayeni wani asibiti mai zaman kansa inda suka ƙi amsar shi, a wannan yanayi ne ya rasa jini mai yawa, har takai ga ya mutu.
Yace: "Muna cikin baƙin ciki, ace mutumin da ba ruwansa kuma mai taimaka wa mutanen shi amma an kashe shi. Wannan babban rashi ne ga kwalejin mu da kuma al'ummar yankin."
A wani labarin kuma Buhari Ya Ɗau Zafi, Ya Sake Bada Umarnin Harbi Akan Duk Wanda Aka Kama da AK-47
Shugaba Buhari ya sake jaddada dokar sa ta duk mutumin da aka kama da AK-47 a harbe shi.
Buhari ya sake faɗin haka ne yayin da yake miƙa wasu kayan aiki ga rundunar yan sandan jihar Lagos.
Asali: Legit.ng