Yan Bindiga Sun Sace Jariri Ɗan Shekara 3 Tare da Matan Aure 5 a Abuja

Yan Bindiga Sun Sace Jariri Ɗan Shekara 3 Tare da Matan Aure 5 a Abuja

  • Wasu yan bindiga sun kutsa har cikin gida a Anguwan Epe, sun yi awon gaba da jariri tare da mata 5
  • Wani mazaunin yankin, Ishaku, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace maharan sun zo cikin shiri
  • Rahoto ya nuna cewa sai da yan bindigan suka gama aikin su sannan jami'an yan sanda suka ƙariso yankin

Yan bindiga sun sace wani jariri ɗan shekara uku tare da mata 5 a Anguwar Epe, bayan sakandiren gwamnati (GSSS) Tungan Maje, Abuja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Sheƙe Sufetan Ofishin

Wani mazaunin yankin mai suna, Ishaku, yace lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:23 na ranar Talata.

Ishaku ya bayyana cewa maharan sun shiga Anguwan cikin dabaru, inda suka fara harbi a sama domin su hana maƙota da jami'an tsaro kawo ɗauki.

Yan bindiga sun kai hari Abuja
Yan Bindiga Sun Sace Jariri Ɗan Shekara 3 Tare da Matan Aure 5 a Abuja Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Yace: "Yan bindigan sun shigo Anguwan daga jikin wani babban dutse dake bayan Epe, suna zuwa suka raba kansu gida-gida, kafin daga baya wasu tawagar sun kutsa cikin wani gida inda suka yi awon gaba da jariri ɗan shekara 3 da mata 5."

Ya ƙara da cewa kafin jami'an yan sanda su ƙariso yankin tuni yan bindigan sun gama aikin su, sun tafi da waɗanda suka yi niyyar sace wa.

KARANTA ANAN: Buhari Ya Ɗau Zafi, Ya Sake Bada Umarnin Harbi Akan Duk Wanda Aka Kama da AK-47

Legit.ng hausa ta gano cewa Tungan-Maje dake kan hanyar zuwa Zuba-Gwagwalada na cigaba da fuskantar matsi daga yan bindiga.

Kakakin hukumar yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, ta nemi a tura mata saƙo maimakon kiran waya, amma har yanzun ba ta turo amsar saƙon da aka tura mata ba.

A wani labarin kuma Ku Gyara Halinku, Ku Tabbatar da Tsaro a Najeriya Idan Kuna Son Aikin Yi, Buhari ga Matasa

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ga gargaɗi matasan Najeriya da su gyara halin su idan suna son aikin yi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Buhari ya faɗi hakane yayin wata fira da yayi da kafar watsa labarai ranar Alhamis da safe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262