Buhari Ya Ɗau Zafi, Ya Sake Bada Umarnin Harbi Akan Duk Wanda Aka Kama da AK-47

Buhari Ya Ɗau Zafi, Ya Sake Bada Umarnin Harbi Akan Duk Wanda Aka Kama da AK-47

  • Shugaba Buhari ya sake jaddada dokar sa ta duk mutumin da aka kama da AK-47 a harbe shi
  • Buhari ya sake faɗin haka ne yayin da yake miƙa wasu kayan aiki ga rundunar yan sandan jihar Lagos
  • Yace gwamnati zata kare lafiya da dukiyoyin yan Najeriya kamar yadda kundin tsarin mulki ya ɗora mata

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ƙara jaddada umarninsa ga jami'an tsaro da su harbe duk wanda suka gani ɗauke da AK-47 ko wani makamai, kamar yadda dailytrust ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ku Gyara Halinku, Ku Tabbatar da Tsaro a Najeriya Idan Kuna Son Aikin Yi, Buhari ga Matasa

Buhari ya sake jaddada dokar ne yayin da yake miƙa kayan aikin jami'an tsato ga hukumar yan sandan jihar Lagos ranar Alhamis, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari
Buhari Ya Ɗau Zafi, Ya Sake Bada Umarnin Harbi Akan Kowa Aka Gani Ɗauke da Makami Hoto: @MuhammaduBuhari
Asali: Instagram

Yayin taron mika kayan aikin, Buhari ya sha alwashin ɗaukar tsattsauran mataki a kan kowaye aka kama yana da hannu wajen kaiwa jami'an tsaro hari.

Yace duk wata ƙasa da ta bari aka maida jami'an yan sandan ta da kayayyakin gwamnati wurin rikici da kuma salwantarwa to ta kama hanyar ruguje wa.

KARANTA ANAN: Yaƙi da Cin Hanci a Mulkin Demokaraɗiyya Yana da Matuƙar Wahala, Buhari

A wani sashen jawabin shugaban, yace:

"Duk da karuwar yawan ƙalubalen da muke fuskanta, Inasan yan najeriya su sa a ransu cewa gwamnati zata kare ƙasarta, zamu kare duk wani abu da yake mallakin gwamnati."

"Zamu kare hanyoyi, zamu kare ƙauyuka da dazuzzuka, sannan zamu tsare rayuwar al'ummar mu."

"Gwamnatin tarayyata ta shirya kuma dagaske take kamar yadda kundin tsarin mulki ya ɗira mata, zata kare lafiya da dukiyoyin yan Najeriya."

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Fallasa Shirin da Aka Yi Don Hamɓarar da Gwamnatinsa

Shugaban ƙasa Buhari yayi iƙirarin cewa zanga-zangar #EndSARS an shirya ta ne don a hamɓarar da gwamnatinsa.

Shugaban ya bayyana haka ne yau Alhamis da safe, yayin fira da kafar watsa labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel