Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Amince da Naɗin Sabon Darakta Janar Na NBC

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Amince da Naɗin Sabon Darakta Janar Na NBC

  • Shugaba Buhari ya amince da naɗin Balarabe Shehu Ilelah, a matsayin sabon Darakta janar na hukumar NBC
  • Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da ministan labarai, Alhaji Lai Muhammed, ya fitar yau Jumu'a
  • Ya kuma bayyana cewa sabon daraktan na NBC zai jagoranci hukumar na tsawon shekara 5

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amice da naɗin, Balarabe Shehu-Ilelah, a matsayin sabon darakta janar na hukumar kula da kafofin watsa labarai ta ƙasa (NBC), kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Sace Jariri Ɗan Shekara 3 Tare da Matan Aure 5 a Abuja

Legit.ng hausa ta gano cewa, sabon daraktan NBC, Balarabe Shehu-Ilelah, kwararre ne a ɓangaren watsa labarai.

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Amince da Naɗin Sabon Darakta Janar Na NBC Hoto: @bashirahmad
Asali: Instagram

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, shine ya sanar da naɗin a wata takarda da kakakin ministan, Segun Adeyemi, ya fitar ranar Jumu'a a babban birnin tarayya Abuja.

Takardar ta bayyana cewa sabon darakta janar ɗin zai jagoranci hukumar NBC na tsawon shekaru 5 a zangon farko, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Buhari Ya Ɗau Zafi, Ya Sake Bada Umarnin Harbi Akan Duk Wanda Aka Kama da AK-47

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan Buhari ya koma Abuja daga jihar Lagos, inda yakai ziyarar aiki ta kwana ɗaya.

A yayin ziyarar, shugaba Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka da suka hada da titin jirgin kasa mai nisan kilomita 157 a filin jirgin kasa na Mobolaji dake Ebutte Metta, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Fallasa Shirin da Aka Yi Don Hamɓarar da Gwamnatinsa

Shugaban ƙasa Buhari yayi iƙirarin cewa zanga-zangar #EndSARS an shirya ta ne don a hamɓarar da gwamnatinsa.

Shugaban ya bayyana haka ne yau Alhamis da safe, yayin fira da kafar watsa labarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262