Wata sabuwa: Makiyaya sun sace fasinjoji 15 a jihar Imo
- na zargin makiyaya da yin awon gaba da wasu fasinjoji a wani yankin jihar Imo a kudancin Najeriya
- An ce sun yi garkuwa da mutane 15 dake cikin wasu motocin bas biyu dake kan hanyar su ta tafiya
- Wani ganau ya bayyana cewa, 'yan bindigan sun zarce da mutanen zuwa cikin daji, masu kuwa sun tsere
An shiga fargaba a Eke-Onuimo, a karamar hukumar Onuimo ta jihar Imo biyo bayan sace fasinjoji 15 a kan hanyar Enugu zuwa Fatakwal da wasu da ake zargin makiyaya ne suka aikata, Sahara Reporters ta ruwaito.
Fasinjojin na tafiya ne a cikin wasu bas biyu daban-daban lokacin da makiyayan suka tsayar da su a kan titin Arondizuogu-Okigwe a yankin jihar.
A cewar wani ganau, masu garkuwar sun kora dukkan fasinjojin motar bas din zuwa cikin daji.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana yadda yake bi wajen nada mukaman gwamnati
An gano cewa wasu fasinjoji a cikin motar ta biyu sun yi nasarar tserewa amma har yanzu ba a san inda suke ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.
Har yanzu rundunar ‘yan sanda ba ta ce komai ba kan lamarin kuma kakakin rundunar na jihar, SP Bala Elkana, ba a samu jin ta bakinsa ba.
Sai dai, a rahoton Daily Trust, an bayyana cewa cikin wani bidiyon da ke yawo a kafar WhatsApp, wata mata da ke cikin damuwa ta ba da labarin yadda ta sha wahala a hannun masu garkuwa da mutanen da ta kubuta daga garesu.
"Akwai wasu daga cikinmu da suka duba girman jikinsu suka ce 'wadannan da alamu suna da iyaye masu arziki'. Na gaya musu cewa ina da ciki, shi ya sa suka kyale ni.”
KU KARANTA: Buhari bai hana Twitter ba, APC ta bayyana manufar shugaban kasa
A wani labarin daban, Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo, ya ce idan doka ta yarda, zai gwammace jami'an bangan Amotekun, su dauki bindigogin AK-47 don bunkasa ayyukan tsaro, The Cable ta ruwaito.
Gwamnan ya fadi haka ne a jawabin da ya gabatar a garin Ibadan ranar Talata a wajen bude taron dimokiradiyya na kasa mai taken, "Makomar dimokuradiyya a Najeriya."
Gwamnan ya ce nasarorin da kungiyar ta samu ya zuwa yanzu ya samo asali ne daga tsarin daukar ma'aikata wanda ya tabbatar da cewa an zabi masu gudanar da aikin daga manyan hukumominsu.
Asali: Legit.ng