Yaƙi da Cin Hanci a Mulkin Demokaraɗiyya Yana da Matuƙar Wahala, Buhari
- Shugaba Buhari ya koka da wahalar yaƙi da cin hanci da rashawa a mulkin demokaraɗiyya
- Shugaban yace tun sanda aka zaɓe shi a matsayin shugaba shekara 6 da ta wuce yake shan wahala wajen yaƙar masu cin hanci
- Hakanan Buhari yayi tsokaci kan yadda gwamnatocin jihohi ke tafiyar da kuɗaɗen kananan hukumomi
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa yaƙi da cin hanci da rashawa a mulkin demokaraɗiyya yana da wahala sosai a samun nasara, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Fallasa Shirin da Aka Yi Don Hamɓarar da Gwamnatinsa
Shugaban ya faɗi haka ne a lokacin wata tattaunawa da gidan talabijin na 'Arise TV' wanda aka haska ranar Alhamis, kamar yadda premium times ta ruwaito.
A cewarsa, yana shan wahala sosai wajen yaki da cin hanci da rashawa tun sanda ya amshi madafun iko a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a mulkin demokaraɗiyya shekara 6 da suka gabata.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta samu nasara wajen bankaɗo masu cin hanci da rashawa daga cikin ma'aikatan gwamnati ba tare da yayata labarin ga yan ƙasa ba.
Buhari yace a lokacin da yake shugaba a mulkin soja, gwamnatinsa ta samu nasara mai ɗumbin yawa a ɓangaren yaƙi da cin hanci.
"A lokacin an hukunta mutane sosai inda aka tura su gidan gyaran hali, kafin a kifar da gwamnatin mu," inji shi.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ku Gyara Halinku, Ku Tabbatar da Tsaro a Najeriya Idan Kuna Son Aikin Yi, Buhari ga Matasa
Buhari ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda gwamnatocin jihohi ke tafiyar da ƙananan hukumomin jihar su, inda yace yadda kasan babu gwamnatin kananan hukumomi a ƙasar nan.
Shugaban yayi nuni zuwa yadda gwamnoni ke handame kuɗaɗen kananan hukumomi, yace: "Babu adalci a tura ma karamar hukuma Naira Miliyan N300m amma miliyan N100m kacal zata isa gare ta."
A wani labarin kuma FG Ta Kafa Sabbin Sharuɗda 3 Kan Twitter, Facebook da Instagram Ko Ta Hana Amfani da Su
Gwamnatin Najeriya ta kafa wasu sharuɗɗa uku akan duk wata kafar sadarwa dake Najeriya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, shine ya bayyana haka ga manema labarai bayan twitter ya nemi sasanci.
Asali: Legit.ng