Shugaba Buhari Ya Fallasa Shirin da Aka Yi Don Hamɓarar da Gwamnatinsa

Shugaba Buhari Ya Fallasa Shirin da Aka Yi Don Hamɓarar da Gwamnatinsa

- Shugaban ƙasa Buhari yayi iƙirarin cewa zanga-zangar #EndSARS an shirya ta ne don a hamɓarar da gwamnatinsa

- Shugaban ya bayyana haka ne yau Alhamis da safe, yayin fira da kafar watsa labarai

- Buhari yayi kira ga matasa da su gyara halayensu, su taimaka wajen samar da tsaro a Najeriya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yayi ikirarin cewa zanga-zangar #EndSARS da aka yi shekarar da ta gabata an shirya ta ne domin a hamɓarar ɗa gwamnatinsa, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ku Gyara Halinku, Ku Tabbatar da Tsaro a Najeriya Idan Kuna Son Aikin Yi, Buhari ga Matasa

Buhari ya faɗi haka ne lokacin da yayi fira da gidan talabijin na 'Arise TV' ranar Alhamis da safe.

Shugaba Buhari Ya Fallasa Shirin da Aka Yi Don Hamɓarar da Gwamnatinsa
Shugaba Buhari Ya Fallasa Shirin da Aka Yi Don Hamɓarar da Gwamnatinsa Hoto: @BashirAhmad
Asali: Instagram

Shugaban ya ƙara da cewa waɗanda suka gudanar da zanga-zangar sun cire wa masu son zuba hannun jari sha'awar zuwa Najeriya.

Ya kuma zargi zanga-zangar da ƙara durkusar da ɓangaren zuba hannun jari daga ƙasashen duniya, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: An Kashe Mutum 500 Tare da Sace Wasu 201 a Mazaɓar da Nake Wakilta, Ɗan Majalisa

Da aka tambaye shi wane shiri yake na samar da masu zuba hannun jari daga ƙasashen waje zuwa Najeriya, Buhari yace:

"Na amsa wannan tambayar shekarar da ta gabata lokacin da ake zanga-zangar #EndSARS. Kun tuna matasan da suka so suyi tururuwa anan domin su hamɓarar dani daga kan mulki?"

"Ku cigaba da faɗa wa matasa su gyara halayen su, su tabbatar da tsaro a ƙasa. Daga nan ne zamu iya jawo hankalin masu zuba hannun jari da dama."

A wani labarin kuma FG Ta Kafa Sabbin Sharuɗda 3 Kan Twitter, Facebook da Instagram Ko Ta Hana Amfani da Su

Gwamnatin Najeriya ta kafa wasu sharuɗɗa uku akan duk wata kafar sadarwa dake Najeriya.

Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, shine ya bayyana haka ga manema labarai bayan twitter ya nemi sasanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262